Nazari a tsanaki kan saki-auri a Arewa
Wani labari da jaridar Daily Trust ta wallafa a kan jarumin Kannywood Adamu Zango dangane da aurensa, ya ja hankalina matuka. Ganin cewa masana’antar tana fama da matsalar tarbiyya sai ga shi daya daga cikin jarumanta zai yi aure wannan matakin nasara ne ga Kannywood. Sai dai abin kaico labarin ya bayyana auren da cewa […]
Wani labari da jaridar Daily Trust ta wallafa a kan jarumin Kannywood Adamu Zango dangane da aurensa, ya ja hankalina matuka. Ganin cewa masana’antar tana fama da matsalar tarbiyya sai ga shi daya daga cikin jarumanta zai yi aure wannan matakin nasara ne ga Kannywood. Sai dai abin kaico labarin ya bayyana auren da cewa shi ne na shida da jarumin zai yi. Ba tare da dogon karatu ba na yanke hukun cin matar da za ta zama ta shida to za ta tarar da gidan ba kowa, haka kuwa aka yi domin mai kawo rahoton ya tabbatar min da hasashena saboda a halin yanzu jarumin ya saki ragowar matan nasa biyar wata kila kuwa wadansu sun yi wani auren, wadansu da dama sun ta fi tare da ’ya’yansu wadansu kuma sun bayar da su domin a kula da su. Abin da na kasa yarda da shi a ce jarumi kamar Zango wanda ya yi suna wajen soyayya a ce shi yake yi wa kannenmu wannan cutarwa ta sakin aure.
Hakika wannann labari ya dada fito da hali da matsalar zamantakewar aure a Arewacin Najeriya .Matsalar yawan sakin aure ta sanya kannenmu mata a hali na jiran tsammanin sake wani auren a nan gaba. Wannan matsalar ba ta kau ba sai ka ji wata ta sake bulowa, hakan ya jawo da yawa daga cikin kannenmu mata suna zaman jiran tsammani domin wadansu da dama sun yi shekaru da dama ba aure. Wata sabuwa kuma mazan wannan zamani su kuma fatara ta hana su yin aure, sannan magidanta kuma sun fi sun su aure wadanda suka ji ma ba su yi aure ba a kan su auri bazawara.
Abin yana kara girma sama da shekara 20 da suka wuce a nan Arewa, sakin aure ya zama ruwan dare, a yanzu da an yi aure zuwa ’yan kwanaki za ka ji an yi saki musamman ma a cikin birane. Mene ne dalilin faruwar haka?
Akwai dalilai masu yawan gaske da suke jawo faruwar haka.Dalili na farko shi ne a wannan zamanin maza ba sa yin aure don Allah sun fi lura da soye-soyen zukatansu kamar; sai mace mai kama kaza zan aura ba sa la’akari da tarbiyya da addini ,galibin aure a yanzu an fi gina shi ne a kan abin duniya. Matasanmu ba a koya musu zamantakewar aure. Abin da ke ransu kawai rayuwar ta-more.
A ra’ayina Masana’antar Kannywood tana daya daga cikin wadanda suka haifar da wannan matsalar. Mafiya yawan fina-finan da suke wallafawa suna farawa ne da gwagwarmaya a kan soyyaya kuma daga kashe ka ga an nuna masoyan sun yi aure sun shiga dankareren gida ga manya-manyan motoci na alfarma ga kujeru na nuna isa da makamantan abubuwan more rayuwa a cikin gidan. Wannan shi ya jefa kannenmu mata da yawa cikin wannan hadari suna ganin wannan ita ce rayuwa. Mutane irin su Adamu Zango suna da hakkin kawo gyara a cikin wannan balahira ta rayuwar aure , su rika shirya fina-finai wadanda zai koyar da rayuwa ta zahiri kuma su bar abin koyi na zahiri su yi shi a aikace, yin haka zai taimaka kwarai da gaske wajen kawo sauyi a rayuwar aure .
Dole sai mun yarda da shawarar da Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II ya ba mu na kawar da al’adu daga cikin sha’anin zamantakewar aurenmu wadanda suke haifar mana da matsaloli.
Ahmed Ibrahim Gusau, Jihar Zamfar