Nazari Da Sharhin Jawabin Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Tun da farko dai, ga gundarin fassarar jawabin nan cikin Hausa, kamar yadda ya gabatar da shi cikin harshen Ingilishi:  Ya ku ’yan Najeriya! Ina matukar godiya ga Allah da kuma dukkan ’yan Najeriya saboda addu’o’inku. Ina murna da na samu dawowa gida cikin ’yan uwana  maza da mata. A yayin da nake can kasar […]

Nazari Da Sharhin Jawabin Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Tun da farko dai, ga gundarin fassarar jawabin nan cikin Hausa, kamar yadda ya gabatar da shi cikin harshen Ingilishi: 

Ya ku ’yan Najeriya!

Ina matukar godiya ga Allah da kuma dukkan ’yan Najeriya saboda addu’o’inku. Ina murna da na samu dawowa gida cikin ’yan uwana  maza da mata.

A yayin da nake can kasar Turai, a kullum ana sanar da ni abubuwan da suke wakana a gida. ’Yan Najeriya sun kasance cikin hakilon tattauna al’amuransu, amma na shiga damuwa da na ankara da wasu kalaman, musamman a kafafen sada zumunta, wadanda suka yi hannun riga da diyaucin kasa, inda suka rika takala da kawo barazana ga kasancewar kasa daya. Wannan mataki ya yi tsauri da yawa.

A shekarar 2003, bayan na shiga harkokin siyasa, marigayi Cif Emeka Ojukwu ya ziyarce ni a garinmu Daura. Ya zauna da ni fiye da kwanaki biyu, inda muka rika tattauna al’amura daban-daban da suka shafi matsalolin Najeriya har zuwa talatainin dare. Daga karshe mun kitse kudurinmu na cewa kasar nan dole ta ci gaba da dorewa a matsayin guda daya a dunkule.

Hadin kan Najeriya tabbas ne kuma ba zai taba zama karkashe a faifai ba. Ba za mu zura ido ga kangararru su kawo mana tashin hankali ba, alhali idan lamarin ya baci su gudu, su kyale wasu cikin hakilon kawo gyara ba, a sakamakon haka wasu su salwantar da rayukansu.

Kowane dan Najeriya yana da ikon rayuwa, ya gudanar da al’amuransa a ko’ina cikin Najeriya ba tare da cikas ba.

Na yi amanna da cewa mafi yawan ’yan Najeriya sun aminta da wannan batun.

Ba za mu ce cikin korafe-korafen wasu babu gaskiya ba, kowace kungiyar jama’a tana da koke-kokenta. Amma wani abin farin ciki da kaye shi ne, Gwamnatin Tarayya tana ba da dama ga mabambantan kungiyoyin al’umma su furta korafe-korafensu, su hada kai su yi aiki tare domin ganin yadda za a zauna kuma a tsira tare.

Majalisun Tarayya da Majalisun Zartarwa na Jihohi su ke dauke da alhakin tattauna al’amuran kasa tare da daukar matakan da suka dace.

Wani abin da mafi yawan al’ummar kasa suka aminta da shi, shi ne, abu mafi alheri shi ne a zauna tare da juna ya fi a ware.

Haka kuma, ina kalubalantar Hukumomin Tsaro da su kara kaimi, kada su yi sake, kada nasarar da aka samu a watanni 18 a baya ta sanya su yi sanyi.

Ya zama wajibi a yaki ’yan ta’adda da masu aikata laifuka ba tare da gajiyawa ba, har sai an ga bayansu, domin mafi yawanmu mu ci gaba da zama cikin lafiya da aminci.

Saboda haka, za mu kara kaimi mu karfafa yaki da: Tsagerun ’yan Boko Haram da suke kokarin kai farmaki ga raunana. Yaki da masu sata da garkuwa da mutane don amsar kudin fansa. Yaki da fadace-fadace tsakanin manoma da makiyaya. Haka kuma da yaki da fadan kabilanci da wasu karkatattun ’yan siyasa ke rurawa. Duka za mu yi maganinsu.

Daga karshe, ya ku ’yan Najeriya, abin da dukkanmu muka kudurta shi ne, mu kawar da kananan bambance-bambance, mu hada kai mu fuskanci kalubalen da ke gabanmu:

kalubalen inganta Tattalin Arziki. kalubalen tsaftace siyasa da hada kan al’umma. kalubalen tabbatar da aminci da zaman lafiya ga dukkan ’yan Najeriya.

Ina kara jaddada matsayina na sadaukarwa, domin ganin mun samu wadannan nasarori tare da tabbatar da dorewarsu. Ina murna da dawowa gida.

Ina godiya, Allah Ya albarkaci kasarmu abin kauna, Najeriya.

Nazari Da Sharhi:

Kamar yadda muka ga wannan jawabi na Shugaban kasa, babu shakka za mu ankara da cewa babu wani abu mai muhimmanci da Baba Buhari bai tabo ba, musamman dai wanda ke ganiyar tashe a wannan lokaci. Babban jigon jawabin nasa, ya ta’allaka ne kan al’amuran tsaro, domin kuwa sai da ingantaccen tsaro ne ake samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Da ingantaccen tsaro ne ’yan kasa ke samun walwala da bunkasa harkokin kasuwanci da dukkan wasu al’amura na rayuwa.

Shugaban ya nemi ’yan kasa da su yi karatun-ta-natsu, musamman dangane da zaman lafiya da hadin kan al’ummar kasa. Ya bayyana karara cewa masu kokowar raba kan kasa su shiga taitayinsu, domin kuwa ba za a lamunci kitimirmirarsu ba. Ya nuna cewa koma dai mene ne korafin wasu, to a lura da cewa zama a dunkule a matsayin kasa daya shi ya fi alfanu fiye da zama a warwatse.

Ga hukumomin tsaro, ya nemi su mike tsaye su kara aiki wurjanjan domin yaki da ’yan ta’adda, musamman ma ’yan Boko Haram da masu garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa da kuma masu tayar da zaune tsaye ta fuskar manoma da makiyaya. Babu shakka, idan aka samar da tsaro ta wadannan fuskokin, al’ummar Najeriya za ta ci gajiyar duk wani al’amari na rayuwa, kamar kasuwanci, aikin gwamnati, noma da kiwo da sauransu.

Haka kuma, shugaban ya nuna wa al’ummar Najeriya hoton masu jawo fitina. Ya nuna cewa wasu karkatattu ne ke zama su kitsa irin wadannan fitintinu, da zarar abin ya ta’azzara sai su gudu su bar kasar, su bar talakawa cikin takaici da asara. Daga karshe wasu mutanen za a bari da kokowar shawo kan al’amarin, wanda ba abu ne ba mai sauki, domin za a yi asarar rayuka da dukiya da sauransu. Don haka, maganin kar a yi, to kar a fara!

Babban abin la’akari dai shi ne, wannan shugaba babu abin da ke zuciyarsa illa kishin kasa da kishin al’ummar kasa. Babu abin da yake da muradi, musamman idan aka yi la’akari da shekarunsa da yanayin illa a samu natsuwa a kasa, a samu tabbatar da gaskiya da adalci, a samu ci gaban kasa, tattalin arziki ya inganta, a samu walwala da wadata. Allah sa mu dace, amin!