Nazari da tambihin kalaman kyautata rayuwa (3)
Tubali na uku, kamar yadda za mu nazarta, shi ne kalmar ‘doyi.’ Shi doyi wani irin yanayi ne marar dadi da ke bayyana, wanda za a iya ji ta shaka a hanci. Daidai yake da wari, wato kishiyar kamshi ke nan. Tunda mun yi fashi bakin tubalan da suka gina wannan bayani na hikima da […]
Tubali na uku, kamar yadda za mu nazarta, shi ne kalmar ‘doyi.’ Shi doyi wani irin yanayi ne marar dadi da ke bayyana, wanda za a iya ji ta shaka a hanci. Daidai yake da wari, wato kishiyar kamshi ke nan.
Tunda mun yi fashi bakin tubalan da suka gina wannan bayani na hikima da muka nazarto, yanzu kuma za mu shiga ma’anar kalamomin gaba daya. A nan, abin fahimta daga bayanin nan shi ne, iyaka hakuri da dawainiyar da za a yi da bako shi ne kwana uku. Da zarar ya wuce kwana uku, ya zama kunci da lalura ga mutane. Don haka, idan za ka yi bakunci, ka tabbatar kada ka wuce kwanaki uku, domin iyaka adadin lokacin da za ka samu farin cikin bakuncinka daga mai masaukinka ke nan. Idan kuwa ka zarce kwana uku, to babu shakka za ka ga canjin yanayi da canjin fuska daga mai masaukinka. Domin ita rayuwa, ’yar kula ce, dole sai mun kula da abin da zai je ya zo, domin kauce wa kuntata wa rayuwarmu da rayuwar abokan zumuncinmu.
Ga kuma bayani na gaba, wanda shi ma wani masani ne mai suna Robert Green ya furta shi, inda ya ce: “Kada ka kuskura ka fi maigidanka ado.” Wadannan kalmomin gargadi ne da ya kamata mu nazarce su, domin tsintar tasirin da ke kunshe a cikinsu. Babban abin da ake nufi da wannan bayani ko gargadi shi ne, kada ka fi mai kora shafawa.
Kai ne kana a matsayin yaron gida ga wani attajiri, wanda ta hannunsa kake samun dan abin rayuwa. Sai ya zamanto shi yana sanya sutura marar tsada, ko kuma matsakaiciya, kawai sai ya wayi gari ya ga kana kece-raini da sutura mai tsananin tsada da kyau fiye da tasa. Me kake jin zai faru a nan? Babu shakka, ka tono matsala ga kanka, domin ko bai ce maka komai ba, mutane za su rika lura da kai-komonka, za su shiga tsegumi da sharhi kan rayuwarka. Balle yana da wuya maigidan nan naka ya ce zai sanya ido kawai, alhali yana ganin kana kece-raini da dukiya fiye da shi mamallakinta. Ko ba komai dai zai shiga taitayinsa domin kare kansa daga halayenka.
Kai ne kake nema a karkashin wani mutum, shi yana hawan babur, sai a wayi gari ya samu ka sayi motar alfarma, kana yin wandaka da warisa a cikinta. Anya wannan shiri zai yi armashi kuwa? Ba na zaton za a samu daidaito da shiriya a tsakani, domin kuwa mutumin nan ba zai samu sukuni da kwanciyar hankali da wannan al’amari ya ci gaba da gudana ba. Zai ga kamar ka zama barazana ne gare shi.
Darusssan da za mu iya koyo na rayuwa daga wadannan muhimman kalamai su ne, mu kula da rayuwarmu ta yau da kullum. Mu rika yin aiki da hankali wajen kiyaye hakkokin abokan zamanmu, domin a samu maslaha da zaman lafiya da lumana a tsakani. Domin ita rayuwar nan, wata aba ce mai wuyar sha’ani, mai bijiro da al’amura mabambanta. Ke nan sai mun yi taka-tsantsan da yadda muke gudanar da al’amuranmu a cikinta, idan ba haka ba kuwa za mu ci karo da akasi; wanda ba shi ne abin bukata ba.
Idan mun duba ginshikan jigogin bayanan hikima biyu da muka tattauna a yau, za mu gane cewa idan muna son kyautata zamantakewa tsakaninmu da mutane, to mu kiyayi jawo abin da zai kuntata musu. Misali, idan za mu je bakunci, to kada mu sake mu dora wa masu masaukinmu nauyin da zai wuce na kwanaki uku. Domin da zarar mun zarce kwanaki uku, to mun shiga hakkinsu. Idan muka duba kalamin hikima na biyu kuma da muka nazarta, wato inda muka ci karo da gargadin cewa kada ka sake ka fi maigidanka ado, shi ma wannan gargadi, yana dauke da darasi mai kima da muhimmanci, wanda ke ishara da kawo tsarin zamantakewa cikin lumana a tsakanin al’umma. Abin da yake nuna mana shi ne, mu yi rayuwa daidai-ruwa daidai- kurji; wato mu daina wuce makadi da rawa, kuma kada mu fi mai kora shafawa.
Sai kuma makon gobe, idan Allah Ya kai mu. A huta lafiya!