Nazari da tambihin kalaman kyautata rayuwa (7)
Assalamu alaikum, ya ku ma’abuta karanta wannan mashahurin fili na Sinadarin Rayuwa. Bayan haka, yau mako na bakwai ke nan da muke nitso da ninkaya cikin tambihi kan wasu fitattun kalamai da wadansu magabata masu hikima da fasaha suka ambata a lokuta mabambanta. A wannan makon ma, za mu nazarci wasu daga irin wadannan kalamai […]
Assalamu alaikum, ya ku ma’abuta karanta wannan mashahurin fili na Sinadarin Rayuwa. Bayan haka, yau mako na bakwai ke nan da muke nitso da ninkaya cikin tambihi kan wasu fitattun kalamai da wadansu magabata masu hikima da fasaha suka ambata a lokuta mabambanta. A wannan makon ma, za mu nazarci wasu daga irin wadannan kalamai da nufin samun daidaito da natsuwa a rayuwarmu. Babbar fa’idar dai ita ce, Allah Ya yi mana gamo-da-katar, wajen cin nasara a nan duniya da kuma babban gidan da muka nufa.
Da farko, bari mu fara nazarin kalamin wani mai hikima, wanda ya ce: “A rayuwa, kada ka ba da umarnin hukuncin da ka san ba za ka iya zartarwa ba.” Idan mun bi kadin wannan kalami, za mu tsinci tubala kamar uku, muhimmai da suka tada ma’anoni da hikimomin da ke cikinsa.
Tubali na farko shi ne ‘rayuwa.’ Ba sai an kai ruwa rana ba kuma ba tare da raba daya biyu ba, an san dai ma’anar rayuwa, wato yadda rayukanmu ke shudawa da wakana cikin zamanmu na duniya a yau da gobe. Tubali na biyu kuwa shi ne ‘umarni.’ Ma’anar wannan kalma, kamar yadda ta fito a cikin gundarin kalaman hikima da muka ambato a sama ita ce, ana nufin mutum ya bukaci a aiwatar ko a zartar da wani abu, ya alla na zahiri, idan na aiki ne ko kuma na bin wani sharadi. Tubali na uku kuwa shi ne ‘zartarwa.’ A takaice, zartarwa na nufin gudanarwa ko aikatawa ko tabbatarwa da sauransu.
Ko ta yaya za mu gano gundarin ma’anar da ke cikin wannan kalami? Abin da za mu yi ke nan, musamman domin mu fa’idantu da hikimomin da ke kunshe a cikinsa. Kai- tsaye, wannan kalami na gargadi ne ko yin ishara ga duk wanda ya samu kansa bisa wani shugabanci cewa ya tsaya tsam da ransa domin nazarin duk wani hukunci da zai ba da ga na kasa da shi domin gudanarwa ko zartarwa.
Idan muka duba lungu da sako na rayuwarmu ta yau da kullum, ana samun shugabanni da shugabanci a ko’ina, kuma a sakade-sakade na rayuwarmu ta yau da kullum. Akwai shugabanci babba akwai matsakaici da kuma karami. Misali, a can kololuwar tsanin shugabanci, ana samun Shugaban Kasa, ga Gwamna ga Shugaban Karamar Hukuma. A yanki ko unguwa kuwa, akwai kansila. Idan muka sauko kasa kuwa, wato muka shiga cikin gidan iyali, akwai uba, akwai uwa, akwai wa ko ya da sauransu. Wadannan duk misalai ne na shugabanni. Idan muka sake duba wani sashin kuma, a ma’aikatu da wuraren sana’o’i, duk wanda ke saman wani ko wadansu da ke aiki ko sana’a a karkashin mutum, to ya zama ko ta zama shugaba.
Idan mun gamsu ko mun fahimci wadannan misalai na shugabanni, to wannan kalami na mai hikima na sama da su yake kai-tsaye. Kada Shugaban Kasa ya ba da umarnin cewa a yi kaza, alhali ba zai jajirce ya tsaya kai-da- fata don ganin ya zartar ko ya gudanar da wannan umarni ba. Haka shi ma Gwamna a jiharsa, ko shugaban karamar hukuma a yankinsa, ko kansila a unguwarsa. Haka ma maigida a gidansa, kada ya ba da umarnin wani hukunci cikin gidansa a yau, an jima kuma ya warware shi ba tare da wani dalili ba, ko ya yi sako-sako wajen zartar da shi.
Za mu ci gaba