Nazari da tariyar manyan fina-finai 20 da suka yi tasiri a duniya
A yayin da duniyar fina-finai ke kara habaka, Aminiya ta gudanar da binciken wasu manyan fina-finai da aka gabatar a ’yan shekarun nan, inda ta tsamo wasu manyan fina-finai guda 20 da suka yi tashe a tsakanin 2011 zuwa bana. Ga sakamakon: 1-Harry Potter and the Hallows (Part Two)Wannan wani kayataccen fim ne da ya […]
A yayin da duniyar fina-finai ke kara habaka, Aminiya ta gudanar da binciken wasu manyan fina-finai da aka gabatar a ’yan shekarun nan, inda ta tsamo wasu manyan fina-finai guda 20 da suka yi tashe a tsakanin 2011 zuwa bana. Ga sakamakon:
1-Harry Potter and the Hallows (Part Two)
Wannan wani kayataccen fim ne da ya yi tashe a tun daga fitowarsa a 2010. An shirya shi ne a Amurka, kuma ya lashe tsagwaron kudi har Fam miliyan 160. A ranar farko da aka nuna shi a gidajen silima, an samu zunzurutun kudi har Fam miliyan 58. Daga karshe dai an yi cinikin Fam miliyan 849 wajen sayarwa da nunawa a gidajen silima.
2-Transformers: Dark of the Moon
Shi ma wannan fim, yana daya daga cikin fina-finan duniya na Hollywood da suka yi tasiri a duniya. Fim din wanda Michael Bay ya shirya, wanda ke dauke da minti 154 kacal. An kashe tsantsagwaron kudi har Dala biliyan daya wajen shirya shi.
3-Pirates of the Caribbean: On Stranger Tides
Shi ma wannan fim ya samu tagomashi a idanun masu kallon fina-finai a duniya. An kashe kimanin Fam miliyan 96 wajen shirya shi, amma kuma ya rarumo gagarumar riba, inda aka yi cinikin Fam miliyan 668 wajen sayarwa da nuna shi a duniya.
4-Kung Fu Panda 2
Wannan fim shi ne irinsa na farko da aka taba shiryawa a jerin Fina-Finan Biri-Boko (Animated Film). An yi amfani da muryoyin fitattun jarumai wajen hada shi. wadannan jarumai kuwa sun hada da Jack Black da Angelina Jolie da Gary Oldman da Dustin Hoffman da Jackie Chan da Seth Rogan da Lucy Lui da Danny McBride da kuma Jean-Claude ban Damme. An kashe tsabar kudi har Fam miliyan 96 wajen shirya shi, amma kuma aka sayar da shi har Fam miliyan 424.
5-Fast Fibe
Shi ma wannan fim ya taki sa’a, inda ya ci kasuwa a tsanake. Duk da cewa ba mu samu adadin kudin da aka kashe wajen shirya shi ba, amma dai an bayyana cewa an yi cinikin Fam miliyan 401 wajen sayarwa da nuna shi a fadin duniya.
6-The Twilight Saga: Breaking Dawn (Part 1)
Kamar fim din Harry Potter, shi ma wannan fim na The Twilight Saga, an kasa shi gida biyu ne, kuma wannan kashi na daya ya samu gamsassar nasa. Fim din ya samar da ciniki har na zunzurutun kudi Fam miliyan 364. Ana sa ran cewa idan har kashi na biyu ya samu nasara kamar wannan na farkon, to zai samar da gagarumar riba ga masu shirya shi, domin kuwa an kiyasata cewa idan an tallata shi sosai, fina-finan biyu za su samar da ciniki na kimanin Fam bilyan biyu.
7-The Hangober Part II
Wannan fim, Bradley Cooper da Ed Helms da Zach Galifianakis ne suka taka rawa mai armashi a cikinsa. Shi wannan kashi na biyu, ya samu ciniki na Fam miliyan 372, wanda haka ya nuna irin gagarumar nasarar da ya samu.
8-The Smurfs
Wannan fim na The Smurfs yana daya daga cikin fina-finan farko da suka yi tashe a farkon shekarar 2011. Duk da cewa masu kalailaitar fina-finan duniya ba su ba shi wata lamba mai kima ba, amma duk da haka ya samu ciniki mai yawa, domin kuwa an samu Fam miliyan 360 daga gare shi.
9-Cars 2
Wannan fim shi ma ya samu nasara, musamman idan aka yi la’akari da tsagwaron cinikin da ya yi, domin kuwa ya samar da Fam miliyan 353. Wani babban dalili da ya sanya ya samu karbuwa ga ’yan kallo shi ne, an yi amfani da muryoyin fitattun jarumai a cikinsa. Jarumai irin su Owen Wilson da Michael Caine da Emily Mortimer da kuma Eddie Izzard, wanda ana jin ma muryoyinsu ne suka kara wa fim din armashi da farin jini.
10-Rio
Fim din Rio yana daya daga cikin Fina-finan Biri-Boko (Animated Films) da suka samu nasara a 2011. An kashe kimanin Fam miliyan 90 wajen shirya shi, amma an yi cinikin Fam miliyan 310. Ya samu nasara sosai, musamman ganin cewa an yi amfanin muryoyin fitattun jarumai, kamar Jesse Eisenberg da Anne Hathaway da Jermaine Clement da Jamie Fodd da Leslie Mann wajen shirya shi.
11-Don 2
Fim din Don 2, ya ci kasuwarsa a 2011. Farhan Akhtar ne ya ba da umurni a cikinsa, a yayin da Shah Rukh Khan da Priyanka Chopra da Boman Irani ne suka jagoranci taurarinsa.
12-Sherlock Holmes: A game of Shadows
A wannan fim din, Guy Ritchie ne ya ba da umurni. Wadanda suka fito cikinsa kuwa sun hada da Jude Law da Noomi Rapace da Jared Harris da sauransu.
13-Mission Impossible: Ghost Protocol
Shi ma wannan fim ya ciri tuta kuma yana daya daga cikin fina-finan duniya da suka samu nasara. Wanda ya ba da umurni shi ne Bard Bird, a yayin da ’yan wasan da suka fito a cikinsa suka hada da Tom Cruise da Jeremy Renner da Simon Pegg da sauransu.
14-Tinker Tailor Oldier Spy
Tomas Alfredson ne ya ba da umurni a cikin wannan fim. Gary Oldman da Mark Strong da John Hurt da Colin Firth ne suka fito a matsayin ’yan wasa, tare da wasu taurarin.
15-Ladies bs Ricky Bahl
Wannan fim ya samu aiki ne daga darakta Maneesh Sharma, a yayin da Ranbeer Singh da Anushka Sharma da Dipannita da Aditi da kuma Parineeti da sauransu suka kasance ’yan wasan da suka fito a cikinsa.
16-The Dirty Picture
Masu kula da al’amuran fina-finai sun ba wannan fim babbar lamba cikin jerin fina-finan duniya da suka fito a 2011. Milan Luthria ne ya ba da umurni a cikinsa, a yayin da bidya Balan da Naseruddin Shah da Emraan Hashmi da Tusshar Kapoor da sauransu suka taka rawa a cikinsa.
17-Albin and the Chipmunks: Chip-Wrecked
Mike Mitchell ne ya ba da umurni a wannan fim. ’Yan wasan da suka fito cikinsa kuwa sun hada da Justin Long da Matthew Gray Gubler da sauransu.
18-Pappu Can’t Dance Saala
Wannan fim bai samu yabo mai yawa daga masu kalailaitar fina-fina Indiya ba, amma duk da haka ya samu nasara saboda dimbin masu kallo da suka kalle shi. Darakta Saurabh Shukla ya ba da umuni a cikinsa, a yayin da kuma ’yan wasa binay Pathak da Neha Dhupia da Rajat Kapoor suka taka muhimmiyar rawa a cikinsa.
19-One Day
Shi ma fim din One Day yana daya daga cikin fina-finan da suka shana a bara kuma Lone Scherfig ne ya ba da umurni a cikinsa, a yayin da Anne Hathaway da Jim Sturgess ne suka jagoranci ’yan wasan da ke cikinsa.
20-Kya Yahi Sach Hai
kwararren daraktan fina-finan Indiya, Y. P. Singh ne ya ba da umurni a wannan fim. ’Yan wasa kamar su Ashok Beniwal da Bobby bats da Nilesh Malhotra da sauransu suka taka rawa a cikinsa.