Nazari game da Asibitin Masu Yoyon Fitsari a Jihar Katsina

A wannan makon, Malam Hassan B. Nagado ya yi nazari ne game da ci gaban da ake samu a asibitin kula da masu yoyon fitsari da ke Jihar Katsina:Cutar yoyon fitsari matsala ce wadda kan faro daga  wajen  haihuwa ko kuma yi wa mata  kaciya ko  cire beli na mata. Idan cutar ta samu diya […]

Nazari game da Asibitin Masu Yoyon Fitsari a Jihar Katsina
Nazari game da Asibitin Masu Yoyon Fitsari a Jihar Katsina

A wannan makon, Malam Hassan B. Nagado ya yi nazari ne game da ci gaban da ake samu a asibitin kula da masu yoyon fitsari da ke Jihar Katsina:
Cutar yoyon fitsari matsala ce wadda kan faro daga  wajen  haihuwa ko kuma yi wa mata  kaciya ko  cire beli na mata. Idan cutar ta samu diya mace sai ta zama. Abin gudu da kyama a cikin al’umma. Fitsari zai rika fita daga cikin jikinta; sai ta rika wani irin wari.
Asibitin masu fama da cutar yoyon fitsari da ke garin Babbar Ruga, da ke yammacin birnin Katsina; shi ne asibitin kula da masu yoyon fitsari mafi girma a Yammcin Afrika kuma daya daga cikin wadda ta yi suna a duniya, mafi kwararrun ma’aikata, wanda ya fi yawan magance matsalar cutar, mafi kayan aiki, kamar yadda rahoton Ma’aikatar  Lafiya Ta  kasa ta bayyana.
A wannan asibitin, wanda yake kebe daga cikin jama’a, ana samun masu wannan cutar daga ko’ina a Afirika Ta Yamma, suna zuwa don neman lafiya. Za ka ga wasu an kawo an yasar, ba ’yan uwa sai dai su rika shigowa Katsina suna bara.
Mafi yawan masu wannan cutar, za ka gan su cikin damuwa da sallamawa cewa rayuwarsu ta kare. Za ka ji suna fatar mutuwa da rayuwa. Wasu za su rika riyawa da a ce mutum idan ya kashe kansa ba ya da laifi da sun kashe kansu sun huta.
A 2007, Gwamnati Jihar Katsina ta kafa wata cibiya, wadda za ta rika koyar da masu wannan cuta sana’o’i da yaki da jahilci da karatun addini da kuma daidaita tunaninsu, su sami tabbacin cewa rayuwa na iya komawa sabuwa, bayan jinyar cutar.
An sanya makarantar a karkashin Ma’aikatar Mata Ta Jihar Katsina, aka tsara ta a bisa tsarin kwana ga duk daliban da aka dauka, suna baro asibitin. Kowace shekara, asibitin zai tace wadanda suka cancanta da wannan horo, sai su bar asibitin su koma makaranta da zama. Daga nan za su rika daukar darussan sana’a da na ilimi kuma suna iya tsallakawa su shiga asibiti su amshi magani.
Hajiya Zubaida Aliyu Malumfashi, ita ce shugabar wannan cibiya tun da aka kafa ta. Ta shaida wa marubucin nan cewa, shigowar hukumar MDGS cikin harkar cibiyar ta sauya tare da sake sabon lale na bunkasar ci gaban wannan waje. Ta ce suna da karancin kayan koyon sana’a sai Malam Isiyaku Dikko Shugaban MDGS ya yi wa ilahirin makarantar sabon zubi. Sabbin kayan sana’a irin na zamani kuma ingantattu.
Ta kara da cewa ya karo musu wasu sana’o’i, wato kiwon kaji, noman lambu da kiwon kifi da rini da yin man gyada. MDGS ta karo masu malamai da take biya albashi mai tsoka, ta kuma gina rijiyar burtsatse.
Don kara wa ma’aikatan cibiyar karfin gwiwa, MDGS ta rika ba su wani hasafi a bisa albashinsu. Sannan ta dauki malamai da za su rika koya wa daliban addini da yi musu nasiha da wa’azin da zai kara musu natsuwa. An kara yawan daliban da ake dauka, sannan aka fito da tsarin ciyar da su abinci mai kara lafiya da gina jiki. Ana biyan alawus na Naira dubu bakwai ga kowace daliba. Idan kuma suka zo yayewar, kowace daliba za a kai ta garinsu kuma MDGS ta damka musu Naira dubu hamsin su ja jari.
Duk lokacin da za a yaye su, matar Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Fatima Shema kan sanya a duba abin da daliba ta koya, a saya mata na’urar da za ta yi sana’ar da ta koya.
Shugabar ta ce dayake asibitin ba na Jihar Katsina ba ne, mafi yawan wadanda ake horarwa, ba ma ’yan asalin jihar ba ne, wasu ma daga kasashen Nijar, Kamaru da Ghana suke zuwa.
Daga Janairun da ya gabata, Gwamnatin Tarayya ta karbe wannan asibiti na garin Babbar Ruga da kuma wannan cibiya mai suna Cibiyar Horar Da Masu Cutar Yoyon Fitsari. A yanzu da wadannan wurare suka koma hannun Gwamnatin Tarayya, ko kulawar nan da kuma gata za su ci gaba kuwa? Lokaci ne zai yi hukunci. Fatan kowa shi ne, Allah Ya sa kar habakar cibiyar ta yi baya.