Nazari game da makomar rayuwa
Ya masu bibiyar wannan fili na Sinadarin Rayuwa, Assalamu alaikum. A wannan makon, filin nan ya samu gudunmowa daga Malam Buhari Liman Kudan, [email protected] (07036687648), wanda ya aiko mana da wannan tsokacin:Wani mutum ne shi kadai, yana tafiya a tsakiyar dokar daji, inda babu gida gaba babu gida baya, sai kwatsam ya hango wani shirgegen […]
Ya masu bibiyar wannan fili na Sinadarin Rayuwa, Assalamu alaikum.
A wannan makon, filin nan ya samu gudunmowa daga Malam Buhari Liman Kudan, [email protected] (07036687648), wanda ya aiko mana da wannan tsokacin:
Wani mutum ne shi kadai, yana tafiya a tsakiyar dokar daji, inda babu gida gaba babu gida baya, sai kwatsam ya hango wani shirgegen zaki. Tun daga nesa ya ankara da cewa zakin nan yana cikin yunwa.
Zakin nan ya tunkaro kansa gadan-gadan. Shi kuwa sai ya fara gudu cikin daji, bai san inda yake dosa ba. Bai ankara ba sai ya ji shi rugum, ya fada a cikin wata tsohuwar rijiya. Ya yi sa’a, kafin ya karasa fadawa kasan rijiyar sai ya rike wani itace da ke gefen rijiyar. Shi kuwa zaki sai ya yi zamansa a waje, a bakin rijiyar yana jiransa domin ya fito ya cinye shi.
A lokacin da mutumin nan ke rike da iccen sai ya kawai ya ankara cewa a jikin iccen akwai wadansu beraye suna ta gaigayen tushen shi, sannan da dubawarsa kasan rijiyar sai hangi wata jibgegiyar macijiya ta fasa kai, tana jiransa ya fado ta cinye. Macijiyar yunwa take ji sosai, domin ta kusa shekara ba ta yi katarin samun babban nama irin na ranar ba.
Daga nan mutumin hankalinsa ya tashi, ga shi babu dabara. To, a wannan halin ne ya waiga zuwa jikin bangon rijiyar, sai ya ga ruwan zuma a manne. Kasancewar shi ma yana jin yunwa sai ya sa dan yatsa yana ta lakatar zumar, yana faman sha kuma yana tandar baki.
Da haka ne har mutumin nan ya manta da manyan hadurra guda 3 da ke fuskantarsa. Hadari na daya, ga zaki can a bakin rijiya yana jiransa ya fito ya halaka shi. Hadari na biyu, a kasan rijiya, ga majiciya can ta fasa kai, tana jiran ya fado ta cinye shi. Hadari na uku, ga beraye a lungu suna gaigayen itacen da ya makale a jikinsa. Babu abin da ya mantar da shi wadannan hadurra uku sai zakin zumar nan da yake lakata.
Saboda zumar nan ta shagaltar da shi, kwata-kwata a hankalinsa ya manta da dukkan hadurran nan, har yana ’yan wake-wakensa.
Toh, Malam mai karatu, ko ka fahimta da darussan wannan labarin kuwa? Koda ma ka fahimta, bari mu kara dubawa, domin kuwa abin da ke faruwa da mutumin nan yana nuna irin rayuwar da muke ciki a yau.
Mutumin nan da ke makale a rijiya yana a matsayin dan Adam ne. Zaki kuwa da ke bakin rijiya, yana jiran lokacin fitowar mutum, yana nufin mutuwa ce shi, wadda take biye da mutum ko’ina. Rijiya kuwa tanan nufin rayuwar duniya ce, inda mutum yake makale na dan lokaci. berayen nan da ke gaigayar iccen day a makale, suna a matsayin kwanakin mutun ne a duniya, wadanda a kullum suke raguwa. Zuma kuwa, ita ce kamar dan wani jin dadi na rayuwar da mutum ke samu. Wannan dan jin dadi, shi ke sanyawa ya manta da mutuwa. Ita kuwa macijiya da ke kasan rijiya, tana nufin hukuncin kabari, wanda ke jiran kowa. Idan mutum bai yi aiki na kwarai bay a samu mummunan hukunci. Idan ya yi aikin kwarai kuwa, ya samu hukunci mai kyau.
Da fatan Allah Ya sa mu dace, mu samu gamawa da duniya lafiya. Amin!