Nazari kan karin harajin kudin kiran waya da na ‘Data’
Kara haraji a wannan fanni zai kara kuntata wa jama’a, kan halin da suke ciki a yanzu.
A makon jiya ne Ministar Kudi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Hajiya Zainab Ahmed Shamsuna, ta sanar da kudirin Gwamnatin Tarayya na kara harajin kudin kiran waya da na amfani da fasahar Intanet ta hanyar waya, da a Ingilishi aka fi sani da Data da kashi 5 cikin 100.
Ministar ta sanar da haka ne a taron masu ruwa-da-tsaki a fannin sadarwar wayar salula a Najeriya, inda ta kara da cewa, wannan kari dai dama yana cikin sabuwar Dokar Hada-Hadar Kudade ta Shekarar 2020 (Finance Act, 2020), wanda aka rattaba wa hannu shekara biyu da suka gabata, kuma sanadiyyar tanade-tanadenta ce aka samu karin Harajin Kayayyaki (VAT) daga kashi 5 zuwa kashi 7.5.
- Dalilin Yamma ta Tsakiya na kin tsarin kowa ya ci tuwon gidansu —Edwin Clark
- Real Madrid ta casa Celta Vigo a wasan mako na biyu na La Liga
Hajiya Zainab ta kara da cewa, wannan kari na kashi 5 da za a ci gaba da karba, zai fara aiki ne nan ba da dadewa ba, kuma tuni hukumar da take shugabanta ta sanar da dukkan hukumomin gwamnati da kamfanonin sadarwar da abin ya shafa.
Illa dai ranar da za a fara aiwatar da dokar ce ake kan tattaunawa a tsakaninta da sauran masu ruwa-da-tsaki a fannin sadarwar. Kuma harajin zai shafi kudin kiran waya da na amfani da data.
Abin da wannan ke nufi shi ne, idan ka kira waya, daga cikin kudin da za a cire, akwai wannan kashi 5.
Haka idan ka sayi Data; duk sa’ar da ka yi amfani da shi ana cazarka kudin damar da aka ba ka ta amfani da fasahar Intanet a wayarka, kuma daga cikin kudin da za a caje ka, akwai wannan kashi 5 na haraji.
Ban ji dadin wannan kudiri ba —Ogunbanjo
A nasa bangare, kamar yadda jaridar Daily Trust da sauran jaridun Najeriya suka ruwaito, Shugaban Kungiyar Masu Amfani da Layukan Wayar Salula ta Kasa, wato: National Association of Telecoms Subscribers, Cif Adeolu Ogunbanjo, ya nuna bakin cikinsa da wannan kudiri na karin kudin harajin kiran waya da data.
Ya bayyana cewa akwai rashin damuwa da halin da ’yan kasa ke ciki da kuma yanayin da tattalin arzikin kasa ke ciki ne. Wannan, a cewarsa, ba shi ne lokacin da ya dace da wannan kari ba.
‘Masu zuba jari a fannin sadarwa za su ragu’
A bangaren kamfanonin wayar salula ma, sun bayyana ra’ayi makamancin wannan, inda suka kara da cewa, wannan kari na haraji wani karin nauyi ne ga fannin sadarwa a Najeriya, domin a halin yanzu ma akwai nau’o’in haraji 39 da kamfanonin sadarwa ke dauke da su.
Bayan haka, yawaitar nau’o’in haraji a kan kamfanonin sadarwa na iya kore masu zuba jari a wannan fanni mai matukar muhimmanci ga rayuwar al’umma.
Ba wannan kadai ba, yawaitar haraji na iya sa kamfanoni su rage ma’aikata, don rage dimbin kudin da suke kashewa wajen tafiyar da kamfanin.
Domin wannan kari zai rage adadin lokaci da Data da masu amfani da wayar salula ke saya.
Kai, wasu ma na iya rage adadin layukan da suke amfani da su misali, daga layuka 2 ko 3, zuwa layi 1 kacal.
Hakan ne zai rage adadin kudin shiga ko ciniki da wadannan kamfanoni suke samu a duk wata.
An kiyasta cewa idan wannan sabuwar doka ta karin haraji ta fara aiki, kamfanonin wayar salula za su kara yawan kudin da suke caja na kiran waya a duk minti guda; daga Naira 20 ko kasa da haka da suke cira a yanzu, zuwa Naira 40.
Haka ma, Gigabyte 1 na Data da a yanzu ake saya a kan Naira 1,000 a misali, zai koma Naira 2,500.
Dalilan Gwamnati
Ministar Kudi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziki ta ce dole ne gwamnati ta aiwatar da wadannan sauye-sauye saboda fadada hanyoyin samun karin kudaden shiga don gudanar da ayyukan gwamnati da ayyukan ci gaban kasa.
Wannan ya biyo bayan kudirin Gwamnatin Tarayya ce wajen yaukaka aljihunta ta wasu hanyoyi daban, sanadiyyar rashin tabbas da ke fuskantar kasar nan a fannin kasuwancin danyen man fetur.
Shawarwari
Ta la’akari da halin da tattalinarzikin kasa ke ciki ba wai a Najeriya kadai ba, duniya gaba daya, zai dace Gwamnatin Tarayya ta sake tunani kafin aiwatar da wannan kari na haraji.
Bayan karancin kudi da jama’a ke fama da shi, darajar Naira ta zagwanye bayan hauhawar farashin kaya da muke fama da shi.
A ka’idar tattalin arzikin kasa a nazarce, mafi munin yanayin tattalin arziki da kowace al’umma za ta samu kanta a ciki shi ne, ya zama an samu hauhawar farashin kayayyaki, tare da rashin aikin yi. Wannan yanayi shi ake kira Stagflation.
A yanayi irin wannan kuwa, kamata ya yi hukuma ta tallafa wa al’umma ta dukkan hanyoyin da za ta iya, amma ba kara karbar abin da ke hannunsu ba.
A kasar Amurka misali, dauke haraji ma gwamnati ta yi daga kayayyakin masarufi irin su iskar gas na dafa abinci da sauransu.
Amfani da wayar salula a yanzu ya zama lalura. Akwai layukan wayar salula sama da miliyan 170 masu rai, a Najeriya, a halin yanzu.
Da yawa cikin mutane kan yi amfani da wayar salula wajen kasuwanci da sada zumunci, da neman aikin yi don toshe lalurar rayuwa.
Kara haraji a wannan fanni zai kara kuntata wa jama’a, kan halin da suke ciki a yanzu.
Muna sa ran hukuma za ta dubi wannan lamari da fuskar tausasawa ga al’umma.