Nazari kan littafin Garin Kimba

Mawallafi: Baban Feto (Mai shari’a Mohammed Uthman El-Mainari). Shekarar dabi: Ba a fada ba. Madaba’a: Madaba’ar Amana Printing and Adbert Ltd, Kaduna. Yawan Shafi: 184. Farashi: Ba a rubuta ba. Manazarci: Salihu  Makera   Kittafin Garin Kimba littafi ne da ya ginu kan labarin rayuwar mutanen wani gari da aka addabi mutanensa da fashi da […]

Nazari kan littafin Garin Kimba

Mai shari’a Mohammed Uthman
El-Mainari (Baban Feto)

Mawallafi: Baban Feto (Mai shari’a Mohammed Uthman El-Mainari).

Shekarar dabi: Ba a fada ba.

Madaba’a: Madaba’ar Amana Printing and Adbert Ltd, Kaduna.

Yawan Shafi: 184.

Farashi: Ba a rubuta ba.

Manazarci: Salihu  Makera

 

Kittafin Garin Kimba littafi ne da ya ginu kan labarin rayuwar mutanen wani gari da aka addabi mutanensa da fashi da satar shanu. Kuma littafin ya kunshi Babi 17 duk da cewa a rubuce an nuna yana da Babi 15 ne.

Babi na Daya wanda ya fara daga shafi na 1 zuwa na 5 ya tabo yadda matsalar barayi da fashi da makami ta addabi garin da kewaye, lamarin da ya sa wadansu samarin Fulani makiyaya su biyu, suka fara tattaunawa don nemo mafita. Babban cikinsu Sham’un ne ya fara nuna wa dan uwansa Shehu illar lamarin, inda ya ce akwai bukatar su tunkari mai garinsu da batun. Kuma duk da cewa da farko Shehu bai son jin irin wannan magana, a karshe Sham’un ya shawo kansa ya bar ra’ayinsa na cewa harkar tabbatar da tsaro na hukuma ce kadai.

Babi na Biyu daga shafi na 6 zuwa na 21 ya nuna lamarin barayin nan ya damu jama’ar garin ma, wanda hakan ya sa mai gari da mutane suke kira da Yallabai ya aike wa ’yan majalisarsa su zo don nemo mafita. Cikinsu akwai Limamin Masallacin Gabas, Malam Hamza, wani fitaccen malami a garin kuma mai dimbin ilimin addini da ya taba na zamani kuma mai karfin fada-a-ji sosai.

Malam Hamza wanda wadansu ke kira da Sheikh Hamza ko Abu Muhammad ko Malam Sheikh, yana rayuwa ce da hatta mai dakinsa tana jin dadin yadda yake taya ta kula da yara da harkokin gida.Yakan yi wa matarsa wasanni don nuna mata soyayya, al’amarin da ba a cika samu a kasar Hausa ba. Ko a wannan rana haka ya yi kafin ya shaida mata cewa za su je taro gidan Yallabai don tattauna lamarin barayi da ’yan fashin da suka addabe su.

A fada, Yallabai ya yi dogon bayani kan wannan matsala, ya tunatar da su abin da ya faru yayin zuwan barayin. Ya ce: “Kuma kun san na ba su umarni da su bar nan, kun ji kuma amsar da suka aiko mani.”

A nan Sarkin Malamai cikin zuciyarsa ya tuna abin da ya wakana lokacin da Yallabai ya tura su wajen barayin da yadda suka tozarta su har wani garjejen barawo ya nuna musu Sarkin Barayin mai suna Zoge dan Kachalla, yanzu shi ne shugabansu shi ne mai kasar ba Yallabai ba. Bayan sun isar da sakon Yallabai, Zoge ya ba su sakon cewa: “Ku je ku gaya masa ya shirya ya bar min kasata da mutanena da tsaunukana, in ba haka ba to…”

Bayan tattaunawa an yanke shawarar a tuntubi wani malami Sufi da ke kan tsaunuka, sannan a ware kudi don tara malamai su yi addu’a. Yallabai ya ce ya mika komai a hannun Malam Hamza, inda ya ce a sake rubuta wasikar tunatarwa a kai birni.

Babi na Uku daga shafi na 22 zuwa 24 ya yi bayanin yanayin garin Kimba ne da yadda mutanen garin suke samun kayan bukatun rayuwa da sauransu.

Babi na Hudu daga shafi na 25 zuwa 28, ya yi bayanin yanayin rayuwar barayin da suka damu garin Kimba ne da yadda wanda ya fi karfin wani yake taushe shi a tsakaninsu.

Babi na Biyar daga shafi na 29 zuwa na 64 kuma Malam Hamza ne ya aika Sham’un zuwa ga wancan Sufi da ke kan tsauni yayin da ya aika abokin kiwonsa Shehu zuwa wurin Alaramma Balarabe Jabir da ke Tsangayar Lamorde, kowanne da irin abin da ake bukata daga gare shi.

Shehu ya ci karo da ’ya fashi amma dai wasikar da zai kai ta tsira, shi kuma Sham’un da ya samu wani wuri yana hutawa, sai ya rika tariyar rayuwarsa da yadda ’yan fashin suka hallaka iyayensu yana yaro har zuwa yadda ya hadu da Malam Hamza da Sufi Mukaddas. A karshe ya iske Sufi ya isar masa da sakon Malam Sheikh ya juyo gida.

Babi na Biyar? (Kamata ya yi ya zamo Babi na Shida) da ya fara daga shafi na 65 zuwa 75 ya kunshin labarin yadda ’yan fashin ne suka kai hari kan wani ayarin ango da amarya da aka daura wa aure a garin Kimba a kan hanyarsu ta komawa kauyen Sirko garin su ango, inda barayin suka sace  kaya da amaryar.

Babi na Shida wanda ya fara daga shafi na 76 zuwa 87, ya yi karin haske ne kan yadda Shehu ya isa Tsangayar Lamorde da yadda ya samu ganin Alaramma don isar da sakon da aka ba shi ya kai.

Babi na Bakwai wanda ya fara daga shafi na 88 zuwa 102, ya tabo labarin Madugu Shehu ne wani fitaccen madugu masanin kasuwanci da ilimin taurari da shi ma ya taka rawa wajen gina labarin litttafin a bangaren kasuwanci da shari’a da sana’o’i.

Babi na Bakwai (wanda ya kamata ya zama Babi na Tara) saboda maimaita Babi na Biyar da wannan Babi na Bakwai, wanda ya fara daga shafi na 103 zuwa 121 ya tabo rayuwa ce tare da tariya kan tarihin jagoran ’yan fashin da suka addabi Kimba ne wato Zoge wanda Bafulatanin Rahaji ne daga Fombina. Zoge ya taso ne a fada a matsayin dan bayi, ya taso da kulle-kullen makirci, kuma ya yi wa ’yar sarkin garinsu fyade. Wannan ya sa ya gudu daga garinsu ya shiga daji a karshe ya fada wata maboyar barayi ya zama mamba. Daga nan ya koma karkashin wani babban dan fashi mai suna Baffa Sego wanda ya cece shi daga ’yan fashin da ya fara haduwa da su. Kuma ya horar da shi ya goge wajen iya fada da ta’addanci.

Babi na Takwas wanda ya fara daga shafi na 122 zuwa147, an yi tariya kan asali da tarihin Baffa Sego ne da gwagwarmayar da ya sha da yadda mutanen yankin da ya fito suka goge wajen magunguna da dibbu. Ya kuma tabo yadda wajen neman ilimin aka samu haduwar wasu al’ummu da suka hada da Barebari da Larabawa da Turkawa. Wannan babi kusan a iya cewa an tashi daga kasar Hausa ce aka shiga wata duniya ta daban, inda aka yi doguwar tafiya daga Arewa zuwa Kudu tafiyar da aka hadu da maguzawa masu bautar dodanni har aka musuluntar da su. A karshe kuma aka nuna yadda aka kai wa Zoge kayan da yaransa suka yi fashi tare da amaryar.

Babi na Tara, daga shafi na 148 zuwa 150 ya nuna yadda su Zoge suka fara tsara yadda za su auka wa kasuwa ce bayan isowar wani ayari.

Sai Babi na Goma, daga shafi na 151 zuwa 154, ya nuna yadda Yallabai da mukarrabansa suka hadu don tattauna dabarun da Sufi ya tsara, tare da bai wa kowa aikin da ya kamata ya yi. Su ma su Zoge sun ci gaba da nasu shirin.

Babi na Goma Sha Daya zuwa na Babi na 13, daga shafi na 155 zuwa 172, sun tabo yadda aka ci gaba da shirye-shiryen yaki a tsakanin mutanen garin Kimba da kuma barayi su Zoge a gefe guda. Cikin shirye-shiryen an hilaci barayin aka badda sawu aka nuna Yallabai ba ya da lafiya sannan ga yara ana tura su makaranta suna gudu. Kuma a wannan hali ne Malam Sheikh ya bada fatawar a rika hada sallolin Magriba da Isha’i, saboda an shiga zaman ribadi. Matasa da jama’ar gari suka cika kan dutsen Kimba suna koyon harbi da dabarun fada. Aka raba jama’ar Kimba rukuni-rukuni, sannan aka shiga addu’a, aka nuna kamar saboda rashin lafiyar Yallaba ne, saboda hila irin na yaki.

Kowane bangare yana da ’yan leken asiri, Zoge na samun labari daga Gatari dan Kondo, sai dai Gatari ya kasa fahimtar abin da ke gudana a garin Kimba a karshe. Shi kuma Yallabai na samun labari ta hannun Malam Tsuut wanda Sarkin Baka ya dasa a cikin su Zoge.

Babi na Goma Sha Hudu, ya bayar da labarin yadda shanun da su Soko da Kallu da Chindo da Nyakal suke kiwo ne suka bazama suka nufi dajin da su Zoge suke, wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da matasan Kimba suka nufi dajin da barayin suke a hanyarsu ta fafatawar karshe. Matasan Kimba sun nufi Kadarkon Tsalle su ma su Zoge suka nufi kadarkon a kokarinsu na auka wa Kimba. Sai dai suna isa Kadarkon Tsalle ta Kudu sai suka rika jin rugumniyar da ba su san kanta ba, ashe wadancan daruruwan shanu ne da suka abodare suka nufo kadarkon kuma ganin tawagar barayin bai sa sun dakata ba. Haka suka auka cikinsu ga kunci ga turmutsitsi da matsi suka cakuda da juna suka hallaka na hallakawa suka raunata na raunatawa a tsakaninsu. An nuna a nan zuciyar Zoge ta karaya ya fara tuna ta’asarsa da dogon burinsa mai kama da kawalweniya. Ya ciza baki ya zaburi dokinsa, abin da yake iya tunawa ke nan kafin turmutsitsin ya hada shi ya fita hayyancinsa.

Shanun suna gama wucewa sai ga ’yan doka dauke da makamai sun kai tallafi ga mutanen Kimba, inda suka karasa tare da matasan da suka yi shirin yaki suka kame sauran barayin da suke da sauran numfashi, aka kai su birni aka gurfanar da su a gaban alkali aka yanke musu hukuncin kisa ciki har da jagoransu Zoge.

Hakika wannan littafi ya tabo hakikanin abubuwan da suke faruwa ne, kuma ya tabo abubuwan da suka shafi tarihi da al’ada da addinin mutanen wannan yanki na Arewa. Kuma littafin ya nuna ko ba dade ko ba jima karsheh mugu ba zai yi kyau ba.

Idan aka cire maimaita kanun babi-babi sau biyu da aka yi wato Babi na Biyar da Babi na Bakwai, ’yan kura-kuran da aka samu ba su da yawa, kuma galibinsu suna da alaka da amfani da Hausar Gudduri ce.

Littafi ne da zai debe wa mai karatunsa kewa ya ga abubuwan da suka faru a cikin littafin kamar da gaske ne, inda zai rika auna abubuwan da halin da wannan al’umma take ciki a yau ko ta ratso.

Sai dai ina bayar da shawara ga marubucin littafin Mai shari’a Mohammed Uthman El-Mainari a yi gyare-gyare tare da tsarma hotuna na zane a dukkan muhimman abubuwan da suka faru a cikin littafin kamar na samarin Fulani suna kiwo da zaman fada da na ’yan fashi sun kai hari sun sace amarya da sauransu.

A karshe ina jinjina ga marubucin kan wannan kokari da ya yi, kuma ina fata zai kara fito da wasu littattafan.

Ga jama’a kuma ina fata za su nemi littafin su karanta don debe kewa da nishadantarwa.

Abin alfaharinka wanda ka yi, ba abin  da Allah ko waninka ya yi maka ba:

37 Abin da Allah ne Ya yi maka, kamar rai da lafiya da arziki da girma da kyau da launi da jinsinka.

38 Abin da Allah ne Ya yi maka, haihuwarka a babban gida, na malanta ko dukiya ko mulki ta fuskar iyayenka.

39 Abin da Allah ne Ya yi maka, samun ’ya’ya na kwarai ko mata ko makwabta da dangogi masoyanka.

40 Abin da Allah ne Ya yi maka, samun malami na kirki ko dalibi, da ’ya’ya, ba ka alfahari da su in ba wani kokari naka.

41 Abin alfaharinka wanda ka yi, ba abin da aka yi maka ko aka yi wa wani naka ba, wanda ba wani kokarinka.

42 Abin alfaharinka yin karatunka da yin aiki da shi da kokarinka wurin samun zama lafiya da barin girman kanka.

43 Abin alfaharinka ne ka kasance, ba sakarai kake ba, ka zama mai kamun kai da natsuwa cikin al’amarinka.

44 Abin alfarinka ne barin mummunan zato da kyashi da hassada ga kowa, ka rika karbar uzurin wani kamar yadda kake so a rika karbar naka.

45 Abin alfaharinka ne neman na kanka ta halaliya, wajen aiki da ilimi ko sana’a ko ciniki da makwabtaka.

46 Abin alfaharinka ne a ce ana zaman lafiya da kai ko da ke, mai gaskiya da hakuri da barin taka doka.

47 Abin alfaharinka ne yin biyayya ga Allah da Manzon Allah da kyautata wa iyaya da mata ko miji da barin tsokana ko ramuwa ga mai tsokanarka.

Za a iya samun Malam Mahmud Sabo Wushishi

ta: 08055736329, 08034358678 

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano