Nazari: Yanayin Najeriya da shugabanninta a jiya da yau

A wannan makon, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Malam Buhari Daure (07035986444), ya aiko da mukalarsa mai take a sama. Ga abin da yake cewa game da yanayin Najeriya da shugabanninta:A shekarun da suka shude, bayan Najeriya ta samu ’yancin kai; an samu shugabanni da dama. Wasu sun yi nagartaccen mulki, wasu sun […]

Nazari: Yanayin Najeriya da shugabanninta a jiya da yau

A wannan makon, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Malam Buhari Daure (07035986444), ya aiko da mukalarsa mai take a sama. Ga abin da yake cewa game da yanayin Najeriya da shugabanninta:
A shekarun da suka shude, bayan Najeriya ta samu ’yancin kai; an samu shugabanni da dama. Wasu sun yi nagartaccen mulki, wasu sun yi kama-karya, wasu sun sace kudin kasar, wasu sun yi magudin zabe, sun dora kasar a saitin lalacewa. An kuma samu wadanda suka yi aiki tukuru wajen ganin sun bunkasa tattalin arziki tare da ba ’yan kasa tarbiyyar zama mutane nagari.
A jamhuriyya ta farko, an samu jagorancin Alhaji Abubakar Tafawa balewa, wanda ya samu horon zama malamin makaranta. Bayan ya koyar a makarantu da dama sai ya shiga siyasa, ya tsaya takara a jam’iyyar mutanen Arewa (NPC); inda ya zama dan majalisa a Majalisar Dokokin Arewa. Daga bisani ya kara cin zabe, ya zama wakili a Majalisar Wakilai a Legas. A nan ne aka zabe shi ya zama Firaminista a 1957, yayin da aka samu ’yancin kai ya ci gaba da rike mukaminsa har zuwa lokacin da aka yi masa kisan gilla, a juyin mulkin farko da aka yi a tarihin Najeriya, a 1966.
Gwagwarmayar yakin ’yancin kai ta ga ’yan siyasa irinsu Aminu Kano, Obafemi Awolowo da su Anthony Enahoro. A zamanin ne Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya yi tasiri wajen tafiyar da Arewa gaba, inda shi kadai ya yi ayyukan gwamnoni goma sha tara, ya kawo ingantaccen ci gaba; ya mutu cikin mutunci.
Shugaban da ya fi muhimmanci a lokacin da aka samu ’yancin kai shi ne Dokta Nnamadi Azikiwe, dan zamani ne kuma ya fara aiki a matsayin dan jarida. Ya wayar da kan mutane, kuma ya samu karbuwa a wajen ’yan kasa. Ya yi aiki kafada da kafada da Herbert Macaulay a jam’iyyarsu NCNC. Zik, kamar yadda ake kiransa; shi ne Gwamnan farko bayan Turawa sun sauke tutarsu a ranar 1 ga Oktoba 1960, juyin mulkin Janairu 1966 ya tafi da gwamnatinsa.
Sannan sai Janar Johnson Aguiyi Ironsi, wanda shi ne sojan da ya fara zama Shugaban kasa bayan an samu ’yancin kai. An hambare jamhuriyya ta farko, Ironsi Inyamuri ne kuma mulkinsa ya tabbatar da nasara – Inyamurai a gwamnati, wanda ya sa sauran kabilun suka ga ba a yi da su, hakan ya sa wasu hafsoshi ’yan Arewa suka yi tawayen da ya kashe Ironsi.
An ba Yakubu Gowan jagorancin kasar, shi ne shugaba mafi karancin shekaru da ya mulki Nijeriya, musamman ganin dan Arewa ne kuma Kirista sai aka ga ba shi shugabanci don gamsar da kowane bangaren kasar zai kawo zaman lafiya!
A zama daya Gowon ya fi kowa dadewa a kan karagar mukli. Ya yi shekaru tara, a tsakanin an yi yakin basasa (1967-70). Gowan bai samu damar gina kasar ba a kan tafarkin masana’antu, duk da cewa a wancan lokacin ne Najeriya ta tabbata kasa mai man fetur kuma a karo na farko aka rika samun kudin shiga fiye da kowane lokaci, har shugaban ya ce “kudi ba su ba ne matsalar Najeriya, yadda za a kashe su.”
Ganin halin da kasa ke ciki, ya sa wasu hafsoshi a jagoranci Murtala Ramat Muhammad suka yi juyin dan wake, inda aka sanar da sauya gwamnati a yayin da Gowon ke halartar taron hada kan Afirika a Kamfala, daga can sai ya wuce gudun hijira Ingila.
Murtala ya ba kasar saitin da har yau da tsarinsa ake dogara wajen tafiyar da lamurranta. A cikin dan kankanen lokacin da Murtala ya yi mulki, ya kawo ci gaban da ya hada da dauke birnin tarayya daga Legas zuwa Abuja, ya tsarkake kasar daga cin hanci da rashawa da ke neman zama wata halayya ga ma’aikata.
Bayan an kashe Murtala sai Obasanjo ya hau karagar mulki, inda ya tabbatar da tsare-tsaren da marigayi Murtala ya shirya wa Najeriya kuma bai tsallake ranar da aka gabatar ba da za a ba farar hula jagoranci kasar ba, inda aka yi zabe kuma ya ba Alhaji Shehu Shagari ragamar kasar.
Jamhuriyya ta biyu ta fara da kyakkyawan fata daga ’yan kasa, a yayin da tafiyar ba ta yi nisa ba, mutane suka gane cewa ’yan siyasa sun sa farar riga ne don su sace kudin kasar, ta yadda aka fara wasa da aiki tare da wulakanta wadanda suka kada kuri’u, a yayin da rashin zaman lafiya ya zama ruwan dare, aka mayar da Shugaba Shagari makaho, inda ake abin da aka ga dama da sunan dimokuradiyya. Sai kwatsam a jajibirin sabuwar shekarar 1994 sai sojoji suka yi juyin mulki, inda suka gabatar da Janar Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban kasa.
Gwamnatin Buhari ba ta bata lokaci ba wajen bayyana manufofinta, inda ta fito fili ta nuna za ta yi yaki da rashin da’a tare da farfado da tattalin arziki, cikin haka ne wasu suka rika guna-guni, musamman ganin abin ya shafi su kansu talakawa, domin idan talaka ya jefar da leda ko ya yi fitsari a gefen hanya sai sojoji su rufe shi da duka, sai aka rika addu’a Allah Ya kawo karshen gwamnatin.
Yayin da Babangida ya samu goyon bayan wasu kananan hafsoshi sai suka hambarar da gwamnatin Buhari a bisa hujjar cewa ya yi tsauri, ba ya bin shawara, yana gaban kansa kamar yadda Janar Sani Abacha ya bayyana a jawabin juyin mulkin 25 ga Agusta, 1985.
A daidai lokacin da Babangida ya mayar da gwamnatinsa ta maslaha, sai aka shigo da alfarma tare da fitar da yunifom din soja da saka siyasa a gabansa. A haka ya rika wasa da mutane, har sai da aka yi da gaske kafin ya fita daga Abuja, duk da yadda M.K.O. Abiola ya yi kokarin karbar kasa da ikon dimokuradiyya.
Babangida ya kafa gwamantin rikon kwarya, inda ya bar baya da kura, Shugaba Ernest Shonekan bai wuce watanni uku ba, inda Ministan tsaro Sani Abacha ya hambarar da gwamnatin tare da alkawarin kawo tsaro da farfado da tattalin arziki. A lokacin ne Abacha ya gayyato Buhari don ya rike masa bangaren gina kasa da kudin rarar man fetur (PTF).
A wannan lokacin ne iyalen Abacha da sarkin dogaransa, Manjo Hamza Al-Mustafa suka ci karensu ba babbaka, domin sun tabbatar da cewa sun kauda duk wanda zai zamar wa ubangidansu barazana, har rai ya yi halinsa. A kusan lokaci daya Allah Ya dauke Janar Shehu ’Yar Aduwa, Janar Sani Abacha da Alhaji Abiola.
Aka samu sabon zubi a shugabancin Abdulsalam Abubakar, wanda ya gaggauta ba da mulki tare da debe abin da ya iske. A haka ne wasu manyan Arewa suka gayyato Janar Obasanjo ya zama Shugaban kasa a bisa kyautata wa Yarabawa bayan mutuwar Abiola. A yayin da Cif Obasanjo ya hau sai ya yi gaban kansa.
Shugaba Obasanjo ya nemi ya zarce sau uku, inda ’yan majalisa suka taka masa birki. Haka ya sa ya dauko Gwamnan Jihar Katsina, marigayi Umaru Musa ’Yar-Aduwa don ya zama magajinsa. Wanda ya yi rashin sa’ar mulki domin baya da koshin lafiya, har rai ya yi halinsa. Mataimakinsa Dokta Goodluck Jonathan ya yi sa’ar zama Shugaban kasa, bayan ya samu goyon bayan wasu gwamnonin Arewa.
Tun a wannan lokacin Najeriya tana wani yanayi na tsautsayi. Tabbas ana cikin hadari domin ba wanda ya san makomar kasar, komai na iya faruwa a kowane lokaci! Musamman domin talakawa na kara talaucewa, sannan kasar ta yi duhu! Babu haske balle a gane hanya.
An wayi gari da tawaye da ta’addanci, yayin da ba wanda yake da zaman lafiya a kasar. A hankali tattalin arzikin Arewa ya janye, komai ya koma ana dogaro da Kudu. Daga can ake kawo kayan kasashen ketare, daga can ake samun kudin shigar da ake yin albashi, sannan shugabannin ’yan can ne!
Najeriya ta shiga wani hali da ba ta taba shiga ba a tarihinta, ba wanda ya san hakan zai haifar da da mai ido ko nakasashe, domin barci da munsharin da kasar ta yi, sai ka iske kasashen da ba su isa su ja da jiha daya ba, suna nuna mata yatsa tare da yi mata fintinkau ta fuskoki da dama, musamman wajen shan romon dimokuradiyya.
***
Hidindimun Gizagawa na wannan makon:
A labarin jajantawa, Bagizage mawakin Gizagawa, Adon Tambuwal, Komi da ruwanka na Gizago (07066710888), wan mahaifinsa ne Allah Ya yi wa rasuwa.
Muna rokon Allah Ya jikansa da gafara, amin. – Gizago.