Nazarin kalaman azanci domin kyautata rayuwa (2)
Ya masu bibiyar Sinadarin Rayuwa, assalamu alaikum. Kamar yadda muka faro maudu’inmu mai take na sama, yau ma za mu dara daga inda muka tsaya. A yau za mu duba wannan bayanin, inda shi ma wani mai hikima da balagar harshe ya ce: “Wahala, ita ke haifar da kwazo, a yayin da shagwaba ke kashe […]
Ya masu bibiyar Sinadarin Rayuwa, assalamu alaikum. Kamar yadda muka faro maudu’inmu mai take na sama, yau ma za mu dara daga inda muka tsaya.
A yau za mu duba wannan bayanin, inda shi ma wani mai hikima da balagar harshe ya ce: “Wahala, ita ke haifar da kwazo, a yayin da shagwaba ke kashe kwazo”
Masu hikimar Hausa ma na cewa, dole uwar na ki, a yayin da kuma suka kara da cewa, wahala ko wuya ba ta kisa. Idan muka nazarci wannan bayanin hikima da ya gabata a sama, za mu fahimci tsagwaron sakon da ke cikinsa. A takaice, yana kira ne ga mutane da su mike su yi aiki tukuru, domin neman na kai. Idan mutum ya tashi tsaye, ya yi aiki kamar da azazza, ba tare da jin nauyin jiki ko kasala ba, babu shakka zai kasance mai kwazo; wannan kwazo kuwa zai haifar masa da nasara a rayuwa. Dalili ke nan ma masu hikimar tarbiyyar yara suka ce, ka ki naka, duniya ta so shi, ka so naka, duniya ta ki shi.
A lokacin da wahala ta haifar da kwazo ga mutum, ita kuma shagwaba, za ta lalata wa mutum kwazo ne. Duk mutumin da ya tashi cikin laushi da shagwaba, ya tashi a matsayin dan lele, wanda komai sai dai a yi masa, bai san ya motsa jiki domin neman abin zaman duniya ba, babu shakka ba zai gane muhimmancin nema ba. Domin kuwa bai san zafin neman ba. Idan haka ta kasance, mutum zai zama koma-baya ta fuskar rayuwa, zai zama malalaci, wanda ba zai iya samun wata nasara ba a rayuwarsa.
Duk da cewa Hausawa sun ce, zafin nema ba ya kawo samu, to kuma zaman laushi ba zai iya haifar da komai ba sai daskarewa da mutuwar zuciya. Mutumin da ke son samun nasarar rayuwa, shi ne mai buri, mai kokarin neman cikar burinsa ta hanyar jajircewa da kokari ga duk abin da ya sanya a gaba.
Akwai masu cewa lallai ba sai sun tashi sun nema ba, duk abin da ke rabonsu zai iya zuwa har gida ya same su. Kamar yadda suke daukar ma’anar karin maganar nan da ke cewa, rabon kwado ba ya hawa sama. Su a ganin su, kasancewar kwado a kasa yake rayuwa ko kuma a gefen ruwa, to kuwa rabon nasa yana nan cikin ruwa, ba zai tashi sama ba.
Hakan ba yana nufin kuma mutum ya shantake, ya zauna cikin gida yana jiran rabonsa ya same shi ba. Idan ma haka ne, to kafin mu yarda da wannan bayani, sai mu koma mu duba rayuwar kwado. Shin zama yake kawai abinci yana samunsa alhali yana cikin barci? Faufau ba haka abin yake ba. Ka je bakin rafi ka natsu ka ga yadda kwadi ke neman abinci. Za ka ga sun fito sun kafa tarko, inda kwarin da ke kai komo, suke zama abincinsu. A nan za ka ga kwado ya yunkura, ya kanannado kwaro ko wata karamar halitta da harshensa, ya cinye. Da bai fito daga ruwa ba ya kafa tarko, ya jirayi abincin nasa, ta yaya kake zaton zai samu?
Wannan ya nuna mana cewa ya zama dole mutum ya tashi ya motsa, ya nufi wurin da zai yi aiki ko sana’a, ya tafi gona domin noma da sauran aikin neman abinci da abin rufin asiri. A nan ne zai gamu da irin nasa rabon, domin ya amfana da shi.
Bias la’akari da wadannan bayanai, ya dace mu zizara wa rayuwarmu Sinadarin Rayuwa, musamman ta kasancewa masu neman ilimi, domin kasancewa masu ilimi ba jahilai ba, sannan mu kasance masu aiki tukuru ba shagwababbu ba.
Allah Ya ba mu karfin halin bin tafarkin sahihiyar rayuwa, da samun nasarar al’amuran alherin da muka sanya gaba, amin.
Za mu ci gaba