Nazarin kalaman azanci domin kyautata rayuwa (3)

Tare da gaisuwar mutunci, Assalamu alaikum. Ya ku masu karanta wannan muhimmin fili na Sinadarin Rayuwa, yau kuma za mu ci gaba da kashi na uku na nazarin wasu kalaman da za su kyautata mana rayuwa. Kamar yadda na fada a makon jiya, na ce irin wadannan kalamai da muke bayaninsu, muna tsintsinto su ne […]

Nazarin kalaman azanci domin kyautata rayuwa (3)
Nazarin kalaman azanci domin kyautata rayuwa (3)

Tare da gaisuwar mutunci, Assalamu alaikum. Ya ku masu karanta wannan muhimmin fili na Sinadarin Rayuwa, yau kuma za mu ci gaba da kashi na uku na nazarin wasu kalaman da za su kyautata mana rayuwa. Kamar yadda na fada a makon jiya, na ce irin wadannan kalamai da muke bayaninsu, muna tsintsinto su ne daga wurare daban-daban kuma mutane masu hikima da fasahar magana ne suka furta su a lokuta da zamunna daban-daban. Wasu bayanan ma an same su ne kacokan daga babban littafi (Alkur’ani) ko kuma hadisan Manzon Allah (SAW). Da ma manzon na tsira, ya shaida mana cewa ilimi kayan mumini ne, duk inda ya iske shi, sai ya dauki abinsa kawai.
Bari mu fara da wannan kalamin, wanda wani masani ya fada, inda yake cewa: “Baki kamar kifi suke, bayan kwana uku sun fara doyi.”
Kamar yadda za mu gani, wannan kalami na dauke da tubala kamar uku da ke dauke da ma’anoninsa. Bari mu dauki tubalan daya bayan daya, domin mu fasa bakin ma’anar gundarin kalaman.
Tubali na farko da ya gina wannan bayani, shi ne kalmar ‘baki.’ Baki na nufin wasu mutane da suka sauka a wani wuri da ba mazauninsu ba na ainahi. Watau sun bar wurarensu na zama, sun je wani wurin na daban, ya Allah ko don ziyara ko kuma wani dalili na daban. Ke nan ba nan za su ci gaba da zama ba, komai dadewa, za su koma gidajensu na ainahi.
Tubali na biyu da ya gina kalaman da muka dauko, shi ne kalmar ‘kifi.’ Kifi dai kamar yadda muka sani, wata halitta ce mai rayuwa a cikin ruwa. Jikin kifi na da santsi sosai, kuma da zarar an raba shi da ruwa, to ba zai iya rayuwa mai dadewa ba, zai mutu. Idan ya mutu kuwa, to idan ba cikin kankara aka adana shi ba, babu shakka zai yi wari, akalla bayan kwana uku.
Tubali na uku, kamar yadda za mu nazarta, shi ne kalmar ‘doyi.’ Shi doyi wani irin yanayi ne marar dadi da ke bayyana, wanda za a iya ji ta shaka a hanci. Daidai yake da wari, watau kishiyar kamshi ke nan.
Tun da mun yi fashi bakin tubalan da suka gina wannan bayani na hikima da muka nazarto, yanzu kuma za mu shiga ma’anar kalamin gaba daya. A nan, abin fahimta daga bayanin nan shi ne, iyaka hakuri da dawainiyar da za a yi da bako shi ne kwana uku. Da zarar ya wuce kwana uku, ya zama kunci da lalura ga mutane. Don haka, idan za ka yi bakunci, ka tabbatar kada ka wuce kwanaki uku, domin iyaka adadin lokacin da za ka samu farin cikin bakuncinka daga mai masaukinka ke nan. Idan kuwa ka zarce kwana uku, to babu shakka za ka ga canjin yanayi da canjin fuska daga mai masaukinka. Domin ita rayuwa, ’yar kula ce, dole sai mun kula da abin da zai je ya zo, domin kauce wa kuntata wa rayuwarmu da rayuwar abokan zumuncinmu.
Haka kuma, wannan na nufin cewa duk wani abu da za mu yi, mu nemi ilimi a kansa, mu kuma gane alfanunsa da tasirinsa. Da haka ne za mu iya aiwatar da rayuwarmu cikin fa’ida. Ta haka ne kuma za mu lizimci kiyayen hakkokin juna, yadda za a gudu tare kuma a tsira tare, ba tare da takura wa juna ba.
A nan, idan za ka tafi bakunta zuwa ga wasu, ya Allah wani gari ne ko wata kasa; sa ka yi nazari ka tambayi kanka, shin wace irin ziyara za ka kai? Shin ziyara ce ta zumunci da musabaha da juna ko kuwa ta neman ilimi ce? Ko kuwa za ka tafi da nufin zama ne na aiki ko na wani abu? Idan ka gano irin bakuncin da za ka yi, to lallai ne sai ka tanadi guzuri da abubuwan da za su taimaka maka, har iya zamanka. Idan ziyarar gaisuwa ce, wato zumunci ko makamanciyarta, to ka sani cewa kada ka wuce kwana uku, domin da ka gota wannan adadin, to ba za ka ji dadin bakuncinka ba. Allah sa mu dace, amin.
Za mu ci gaba

Dausayin kauna

Takaddamar Soyayya: Tsakanin Maza Da Mata, Wa Ya Fi Rikon Alkawarin Soyayya? (8)

 

Tafiya sannu-sannu kwana nesa. Ga shi a yau mun kwashe makonni takwas cikin wannan maudu’i, wanda kuma in sha Allah za mu karkare shi a wannan makon. Za mu shiga sabon maudu’i.
Sakon farko na A’isha A. Abdulwahab (08106699206) ne, tana cewa: “Gaskiya idan aka ce rikon alkawari ne ko soyayya, kowa na taka rawar ganinsa, ana samun mata da maza gaba daya da rikon amana sai dai in Allah bai hada ka da nagari ba. Mu dai muna rokon Allah Ya bar mu da masu son mu. Fatan alheri ga ma’abota wannan fili na FDk.”
Sai kuma sakon Hafsat Musa Gombe, tana cewa: “FDk, mata sun fi maza rike alkwarin soyayya. Duk wanda ya ce wai maza sun fi rike alkawarin soyayya bai fadi gaskiya ba, ya fadi son ransa ne. Ai mata su suka fi rike alkawarin soyayya. Idan mace tana son ka don Allah ba abin da zai sanya ta karya alkawarin da ta yi maka.”
Shi kuwa Muhammad Hassan Danbaza, Zamfara Radio Gusau (07068040761), yana cewa: “FDk, da fatar kai da masoyan wannan maudu’i a Dausayin kauna duk kuna lafiya. A gaskiya mata sun fi rikon alkawari a fagen soyayya saboda ba zan manta ba, akwai wata yarinya suna soyayya da wani gaye; kullum ba ta son bacin ransa amma wallahi rana daya ya juya mata baya. Saboda haka yarinyar ta shiga matsala, kullum ba lafiya, tana ta tunaninsa.
“Haka ma akwai wata yarinyar suna tare da wani suna soyayya amma wallahi ranar da ta samu hatsarin mota, aka ce sai an cire mata kafa daya, kawai sai ya juya mata baya kuma ya ki aurenta; doli aka ba da ita sadaka.”
Shi ma Amiru Isa Bakori (08075959086), a nasa ra’ayin yana cewa: “A gaskiya zan iya cewa maza sun fi rike alkawari. Ba wai na ce su ma matan babu ba, a’a, da mazan da matan dukkansu ba a taru aka zama daya ba. Domin ni ma mace ta koya mini hankali amma kuma daga karshe abun sai san barka.”
Zainab Muhammad Chado KMC Jakara (07038121794), tana cewa: FDk, ina yi maka fatan alheri. A gaskiya mata sun fi maza rikon alkawarin soyayya. Ba wai don ina mace ba, mace takan iya rasa komai don ta rike alkawarin masoyinta, takan jira shi ya gama karatu har ya samu aiki. Idan mace tana son ka, duk wata hidima ta aure takan yafe wa namiji idan ba shi da ikon yi, ta ce sadaki kawai take so.”
Sai kuma sakon Umar Muhammad Zariya (08138163499), wanda ke cewa: “FDk, maza sun fi rike alkawarin soyayya, sai dai kuma akwai mata masu rike amana; ba duka suka zama daya ba. Akwai mazan da suma mayaudara ne anma rike alkawari sai maza.”
Ita kuwa Fatima Abuja (08114300018) ta kwaso ta da zafi, inda take cewa: FDk, ai iya yaudara, dadin baki, iya karya kamar kudin duba sai maza. Namiji rigar kaya. Namiji ba a gane gabanka. A roke ka dari biyu a gida, ka ce ba ka da ita, ka je waje ka ba da dubu ko ba a roke ka ba. Ka fadi abin da kake so ta yi maka, anjima ka ce kai wallahi zaman hakuri kake da ita. Ki goya shi a baya ya dawo kuma ya rika zagin bayan. Kadan daga cikin kirarin mugun halayyar maza ke nan.
“Ai duk macen da soyayya ta sa ta dauki namiji a uba, to ta mutu marainiya. Nuna gaskiya da rikon amana a soyayya, wannan sai a wajan mata. Ta nuna tana son sa tsakani da Allah, nan kuma yaudara ce tsantsa a ransa. To maza! Ga dai Ibrahim A. Ibrahim Kano ya gano gaskya, ku ma dai Allah Ya sa ku gano. Ai ni da in fada a cikin taskon sharin da namiji, gara na tsinci kaina a bakin kura, ko ba komai dai na yi mutuwar shahada!”
Daga karshe, za mu rufe wannan maudu’i da ra’ayin Salisu Maliya Kano (08099139741), wanda ke cewa: “FDk, gaskiya mata sun fi rike alkawari. Wallahi akwai abokaina, kowa yana da mata amma kowa yana da wata budurwa a waje kuma ba aure za su yi ba. Akwai wanda nake wa fada kan irin wannan amma abin da ya ce ina kunyar in fada saboda kar mata su fusata. Amma mata da yawansu in suka shiga komar namiji, hmm! Allah Ya gyara, amin.”
***