Nazarin kalaman azanci domin kyautata rayuwa (4)
Tare da gaisuwar mutunci, Assalamu alaikum. Ya ku masu karanta wannan muhimmin fili na Sinadarin Rayuwa, yau kuma za mu ci gaba da kashi na hudu na nazarin wasu kalaman da za su kyautata mana rayuwa. Kamar yadda na fada a baya, na ce irin wadannan kalamai da muke bayaninsu, muna tsintsinto su ne daga […]
Tare da gaisuwar mutunci, Assalamu alaikum. Ya ku masu karanta wannan muhimmin fili na Sinadarin Rayuwa, yau kuma za mu ci gaba da kashi na hudu na nazarin wasu kalaman da za su kyautata mana rayuwa. Kamar yadda na fada a baya, na ce irin wadannan kalamai da muke bayaninsu, muna tsintsinto su ne daga wurare daban-daban kuma mutane masu hikima da fasahar magana ne suka furta su a lokuta da zamunna daban-daban. Wasu bayanan ma an same su ne kacokan daga babban littafi (Alkur’ani) ko kuma hadisan Manzon Allah (SAW). Da ma manzon na tsira, ya shaida mana cewa ilimi kayan mumini ne, duk inda ya iske shi, sai ya dauki abinsa kawai.
Ga kuma bayani na gaba, wanda shi ma wani masani ne mai suna Robert Green ya furta shi, inda yake cewa: “Kada ka kuskura ka fi maigidanka ado.”
Wannan kalmomin gargadi ne da ya kamata mu nazarce su, domin tsintar darussa da tasirin da ke kunshe a cikinsu. Babban abin da ake nufi da wannan bayani ko gargadi shi ne, kada ka fi mai kora shafawa.
Kai ne kana a matsayin yaron gida ga wani attajiri, wanda ta hannunsa kake samun dan abin rayuwa. Sai ya zamanto shi yana sanya sutura marar tsada ko kuma matsakaiciya, kawai sai ya wayi gari ya ga kana kece raini da sutura mai tsananin tsada da kyau fiye da nasa. Me kake jin zai faru a nan? Babu shakka, ka tono matsala ga kanka, domin ko bai ce maka komai ba, mutanen da za su rika lura da kai-komonka, za su shiga tsegumi da sharhi kan rayuwarka. Balle yana da wuya maigidan nan naka ya ce zai sanya ido kawai, alhali yana ganin kana kece raini da dukiya fiye da shi mamallakinta. Ko ba komai dai zai shiga taitayinsa domin kare kansa daga halayenka.
Kai ne kake nema a karkashin wani mutum, shi yana hawan babur, sai a wayi gari ya same ka ka sayi motar alfarma, kana yin wandaka da warisa a cikinta. Anya wannan shiri zai yi armashi kuwa? Ba na zaton za a samu daidaito da shiriya a tsakani, domin kuwa mutumin nan ba zai samu sukuni da kwanciyar hankali da wannan al’amari ya ci gaba da gudana ba. Zai ga kamar ka zama barazana a gare shi ne.
Darusssan da za mu iya koyo na rayuwa daga wadannan muhimman kalamai na rayuwa su ne, mu kula da rayuwarmu ta yau da kullum. Mu rika yin aiki da hankali wajen kiyaye hakkokin abokan zamanmu, domin a samu maslaha da zaman lafiya da lumana a tsakani. Domin dai ita rayuwar nan, wata abu ce mai wuyar sha’ani, mai bijiro da al’amura mabambanta. Ke nan sai mun yi taka-tsan-tsan da yadda muke gudanar da al’amuranmu a cikinta, idan ba haka ba kuwa za mu ci karo da akasi; wanda ba shi ne abin bukata ba.
Idan mun duba ginshikan jigogin bayanan hikima biyu da muka tattauna a yau, za mu gane cewa idan muna son kyautata zamantakewa tsakaninmu da mutane, to mu kiyayi jawo abin da zai kuntata musu. Misali, idan za mu je bakunci, to kada mu sake mu dora wa masu masaukin bakuncinmu nauyin da zai wuce na kwanaki uku. Domin da zarar mun zarce kwanaki uku, to mun shiga hakkinsu. Idan muka duba kalamin hikima na biyu kuma da muka nazarta, watau inda muka ci karo da gargadin cewa kada ka sake ka fi maigidanka ado. Shi ma wannan gargadi, yana dauke da darasi mai kima da muhimmanci, wanda ke ishara da kawo tsarin zamantakewa cikin lumana tsakanin al’umma. Abin da yake nuna mana shi ne, mu yi rayuwar daidai ruwa daidai kurji; watau mu daina wuce makadi da rawa, kuma kada mu fi mai kora shafawa.
Sai kuma makon gobe, idan Allah Ya kai mu. A huta lafiya!