Nazarin kalaman azanci domin kyautata rayuwa (6)
Jama’a masu karatu, Assalamu alaikum. Yau ma dai kamar yadda muka faro makonni hudu da suka gabata, za mu ci gaba ne da fashin bakin wasu kalaman azanci domin kyautata rayuwa da muka ci karo da su a wurare daban-daban. Kamar yadda bayani ya gabata, irin wadannan kalamai na hikima, magabata ne masu fasaha da […]
Jama’a masu karatu, Assalamu alaikum. Yau ma dai kamar yadda muka faro makonni hudu da suka gabata, za mu ci gaba ne da fashin bakin wasu kalaman azanci domin kyautata rayuwa da muka ci karo da su a wurare daban-daban. Kamar yadda bayani ya gabata, irin wadannan kalamai na hikima, magabata ne masu fasaha da hikima da basira suka furta su, mu kuma za mu ci gaba da amfana da su, kasancewar hikima kayan al’umma ce. Allah Ya albarkace mu da dacewa da tasirin kowace hikima, amin.
Kalamin farko da za mu tattauna a kansa a yau, ya fito ne daga bakin wani magabacin mai hikima, wanda ba mu tantance sunansa ba, amma dai ga abin da yake cewa: “Gara ka yi shiru kada a san kai wawa ne, da ka buda bakinka ka tona wa kanka asiri.”
Lallai kam, wannan bayani ya fassara kansa da kansa, kodayake bari mu bi kadinsa domin tsintar darasin da ke kunshe a cikinsa. Kamar yadda al’amura suke gudana, mafi yawan jama’a ba su san cewa magana na da kima da tasiri ba a rayuwa. Abin da ya kamata mu gane shi ne, ita magana wata irin abu ce mai siffa, wacce ke bayyana halaye da kamannin mai yin ta. Idan mutum mai hikima ne da basira da hankali, ta hanyar maganganun da yake yi jama’a za su gane haka. Haka kuma, idan mutum wawa ne, dolo, marar tsinkaya da ilimi, duk dai ta hanyar maganganunsa za a fahimta da haka. Don haka, mu kasance muna kula da abubuwan da muke furtawa na magana, mu rika yin maganganun da suka dace da halayenmu na kwarai, domin kuwa da su ne za a auna mutuncinmu da kamalarmu. Ya fi sauki da fa’ida ga mutum ya kame bakinsa ya yi shiru, maimakon ya ce zai saki baki yana maganar da ba ta da amfani ga rayuwarsa da kuma rayuwar sauran al’umma da ke kusa da shi. Kada kuma mu manta da karin maganar nan ta Hausawa, wacce ke cewa, magana zarar bunu ce, idan ta fita ba ta komawa. Kamar dai yadda wani mawaki ya ce ne, “Malam iya bakinka, in ka kiya ya ja maka…” Haka dai batun yake, domin kuwa bakinka dai shi ne linzaminka.
A lokacin da mutum ya saki baki yana fadin banza da wofi, komai girmansa da kimarsa ga mutane, abu guda za su dauke shi – wawa. Domin kuwa da wadannan kalamai nasa za su yi masa alkalanci.
A nan, domin kauce wa haka, me ya kamata mutum ya yi? Kamata ya yi ka yi wa bakinka linzami. A duk lokacin da ka zo yin magana, ka natsu, ka yi tunanin abin da zai je ya komo. Ka tambayi kanka, shin abin da zan fada, mai kyau ne ko akasinsa? Shin wane tasiri kalamaina za su jawo? Idan ka tabbatar da cewa abin da za ka fada mai kyau ne kuma mai amfani, to sai ka zabi kalamai masu kyau da ilimi, ka furta su.
Babu shakka, idan ka lizimci yin haka, masu saurarenka za su yi maka alkalanci mai kyau, za su shaide ka da cewa kai mutum ne nagari, mai natsuwa da hankali.
Hatta mafificin halitta, Manzo Muhammadu (SAW), ya bayyana mana cewa, idan mun tashi yin magana, to mu fadi alheri ko kuma mu yi gum da bakinmu. Wannan na nuna cewa, sakin baki sakaka wajen fadin kalaman da ba su da amfani ga kai kuma ba su da amfani ga waninka, furta su bai da wani amfani. A irin wannan lokaci, har gara ma ka yi shiru da bakinka, ka fi amfana.
Babban tasirin da ke cikin wannan kalami shi ne, mu gane cewa mu ne za mu sama wa kanmu mutunci a cikin mutane. Babban abin da zai jawo maka mutunci shi ne irin yadda kake mu’amala a cikin al’umma. Kuma babban makamin da ke bayyana mutum shi ne harshe, ma’ana kalaman da kake furtawa a yayin mu’amalarka da mutane. Idan ka rika furta kalaman natsuwa da fahimta da ilimi – haka mutane za su dauke ka, wato mutum mai hankali da natsuwa da ilimi. Idan kuwa ka rika furta kalaman banza da na wauta da na shashanci – haka za su dauke ka, wato mutumin banza, wawa, shashasha.
Allah sa mu dace, amin.