NBC ba ta da hurumin tsara wa ’yan jarida yadda za su yi aikinsu — Amnesty
Amnesty ta yi kakkausar suka kan wannan mataki na NBC.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International, ta yi kakkausar suka ga Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), kan sabon umarnin da ta bai wa kafafen yaɗa labarai.
Ƙungiyar ta ce hukumar ba ta da ikon faɗa wa ’yan jarida yadda za su gudanar da aikinsu.
- Shekarau da Gwarzo sun sauya sheƙa daga PDP zuwa APC
- Fafaroma Leo ya yi tir da danniya da wawason albarkatun ƙasa a Afirka
Babban Daraktan Amnesty International a Najeriya, Isa Sanusi ne, ya yi magana a madadin ƙungiyar, inda ya soki NBC kan ƙoƙarinta na sarrafa ’yan jarida da kafafen yaɗa labarai.
Ƙungiyar ta ce umarnin, wanda ya shafi shirye-shiryen siyasa, al’amuran yau da kullum ba komai ba ne face takunkumi ga kafafen yaɗa labarai.
Amnesty, ta ce wannan mataki na iya sa ’yan jarida da kafafen yaɗa labarai su fara taƙaita kansu wajen fitar da rahotanni, wanda hakan zai cutar da ’yancin aikin jarida da kuma dimokuraɗiyya.
“Kafafen yaɗa labarai na Najeriya masu zaman kansu suna bai wa mutane damar nema, tattaunawa, karɓa da kuma yaɗa bayanai da ra’ayoyi cikin ’yanci kamar yadda Yarjejeniyar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Afirka da Yarjejeniyar Duniya kan Hakkokin Jama’a da Siyasa suka tanada,” in ji Sanusi.
Sanusi, ya kuma buƙaci hukumomin Najeriya da su daina amfani da NBC wajen murƙushe ’yan jarida da kafafen yaɗa labarai masu zaman kansu.
“Dole ne hukumomin Najeriya su daina amfani da NBC a wannan yunƙuri na ci gaba da neman rufe bakin ’yan jarida da kafafen yaɗa labarai waɗanda suke da muhimmanci wajen kare haƙƙin jama’a na samun bayanai,” in ji shi.
Amnesty, ta ce sabon umarnin NBC ya saɓa wa kundin tsarin mulki kuma yana nuna salon mulkin danniya.
Ƙungiyar ta kuma ƙarfafa gwiwar masu watsa shirye-shirye da ’yan jarida a faɗin ƙasar da su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin jarumtaka da ’yanci ba tare da tsoro ba duk da matsin lambar da ake musu.