NCAA za ta tantance ingancin jiragen sama a Nijeriya
Za a gudanar da cikakken bincike kan ingancin jiragen saman domin kiyaye fasinjoji.
Hukumar NCAA mai kula da zirga-zirgar jiragen sama a Najeriya za ta gudanar da cikakken bincike kan ingancin jiragen saman da ake amfani da su a cikin kasar.
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan a wani shirin tashar talabijin ta Channels na jiya alhamis mai taken “Politics Today” a turance.
Ya bayyana cewar baya ga dakatar da ayyukan kamfanin jiragen saman Dana da kuma aikin tantance lafiyar jiragen saman da ake zirga-zirga da su, za a gudanar da bincike akan duk wani kamfanin jirgi da ke aiki a kasar nan domin kiyaye lafiyar fasinjoji da ma harkar sufurin jiragen saman baki ɗaya.
A Larabar da ta gabata ne, Keyamo ya umarci Hukumar NCAA ta dakatar da ayyukan kamfanin jirgin saman Dana, inda ya ce abubuwan da suka same shi a baya-bayan nan sun jawo matukar damuwa game da tsare-tsarensa na kiyaye afkuwar hadurra da ma karfin jarin gudanar da harkokinsa.
Ministan ya ce kamfanin jirgin saman zai ci gaba da kasancewa a dakace har sai an gudanar da cikakken bincike a kansa, umarnin da Babban Daraktan Hukumar ta NCAA, Chris Najomo, ya aiwatar nan take.
An aiwatar da hukuncin dakatarwa kan kamfanin Dana Air sa’o’i 24 bayan da ɗaya daga cikin jiragensa ya kauce daga kan hanyarsa a filin saukar jiragen saman Legas.