NCC: An samu raguwar masu canza layi da mutum dubu 19 da 419 a watan Oktoba
Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) a ranar Asabar da ta gabata ne ta ce ta samu wani rahoto daga kamfanonin sadarwar kasar nan da ya nuna an samu raguwar masu canza layi daga wani kamfanin sadarwa zuwa wani (Mobile Number Portability, MNP) da kimanin mutum dubu 19 da 419 a watan Oktobar bana. Hukumar NCC […]
Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) a ranar Asabar da ta gabata ne ta ce ta samu wani rahoto daga kamfanonin sadarwar kasar nan da ya nuna an samu raguwar masu canza layi daga wani kamfanin sadarwa zuwa wani (Mobile Number Portability, MNP) da kimanin mutum dubu 19 da 419 a watan Oktobar bana.
Hukumar NCC ta wallafa wannan bayani ne a shafin sadarwarta na yanar gizo da take fitarwa daga lokaci zuwa lokaci. Rahoton ya nuna yadda aka samu raguwar masu canza layi daga wani kamfanin sadarwa zuwa wani. Shi dai tsarin canza layi daga wani kamfanin sadarwa zuwa wani, wata dama ce da NCC ta bullo da shi ga duk mai bukatar yin haka. Alal misali mutum yana da damar ya canza layinsa da yake amfani da shi a kamfanin Airtel zuwa na MTN ko akasin haka ba tare da canza ainihin lambobin ba.
Kamar yadda rahoton ya nuna, an samu kimanin mutum dubu 33 da 514 na wadanda suka canza layinsu a watan Satumbar wannan shekara da hakan ta sa aka samu raguwar masu canza layi da kimanin dubu 14 da 095 a watan Oktobar bana.
Rahoton ya ci gaba da cewa daga cikin masu canza layi mutum dubu 19 da 419 a watan Oktoba, dubu 9 da 713 sun canza layi ne a tsarin “Incoming Porting Actibities” yayin da dubu 9 da 706 suka canza layinsu a tsarin “Outgoing Porting Actibities”.
Bayanin ya nuna an samu al’umma dubu 1 da 432 da suka canza layinsu daga kamfanin Airtel zuwa na wasu kamfanonin sadarwa a watan Oktoba. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an samu raguwar masu canza layi a kamfanin Airtel da kimanin dubu 3 da 408 daga kimanin dubu 4 da 840 da suka canza layinsu a watan Satumba.
Hukumar NCC ta ce a watan Oktoba an samu wadanda suka canza layi daga kamfanin MTN zuwa wasu su kimanin dubu 2 da 777 da hakan ya nuna an samu raguwar mutum dubu 1,848 idan aka kwatanta da watan da ya gabata. A watan Satumba an samu wadanda suka canza layinsu daga MTN ne zuwa wadansu kamfanonin su kimanin dubu 4 da 625.
Haka kuma NCC ta ce kimanin mutum dubu 2 da 409 ne suka canza layinsu na GLO zuwa wasu a watan Oktoba da hakan ya nuna an samu raguwar wadanda suka canza layinsu a kamfanin da kimanin dubu 1 da 905 idan aka kwatanta da mutum dubu 4 da 314 da suka canza layinsu a watan Satumba.
A karuwa kuwa, kamfanin 9moble ne ya fi samun karuwar kwastomomin da suka canza layukan sadarwarsu zuwa wajensa inda ya samu mutum dubu 4 da 579 a watan Oktoba.
Kamfanin MTN ne ya zo na biyu inda ya samu karuwar mutum dubu 2 da 394 yayin da kamfanin Airtel ya samu karuwar mutum dubu 1 da 978 yayin da kamfanin GLO ya samu karuwar mutum 762.
Rahoton ya nuna duk da irin matsalolin da suka daibabaye kamfanin Etisalat (wanda yanzu ake kira 9mobile), al’umma da dama sun canza layukansu zuwa 9mobile da hakan ya nuna har yanzu kamfanin yana da tasiri a idon al’umma.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ce NCC ta bullo da tsarin canza layi ne daga wani kamfanin sadarwa zuwa wani tun a ranar 22 ga watan Afrilun 2013 da hakan ta kamfanonin sadarwar suka shiga yin gasa don janyo ra’ayin jama’a.