NCC da CBN za su kulla yarjejeniya game da huldar ciniki ta yanar gizo
Hukumar Kula Da Sadarwa ta kasa (NCC) tare da hadin gwiwar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta ce yanzu haka suna kulla wata yarjejeniya a tsakaninsu da zai ba jama’a dama su rika kulla huldar ciniki ta hanyar saye ko sayar da kaya kuma a biya kudin ta amfani da wayar salula ba tare da an […]
Hukumar Kula Da Sadarwa ta kasa (NCC) tare da hadin gwiwar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta ce yanzu haka suna kulla wata yarjejeniya a tsakaninsu da zai ba jama’a dama su rika kulla huldar ciniki ta hanyar saye ko sayar da kaya kuma a biya kudin ta amfani da wayar salula ba tare da an ziyarci wani banki ba wato (e-transaction). Darakar hulda da jama’a na NCC Misis Helen Obi ce ta sanar da haka.
Ta bayyana haka ne a lokacin da take amsa tambayoyin manema labarai a taron ganawa da al’umma da NCC ta shirya karo na 8 a Abuja.
Taron wanda NCC ke shirya wa tana gudanar da irinsa ne don ganawa da al’umma ne wajen wayar musu da kai da a kan hanyoyin da yakamata su bi a duk lokacin da aka zalunce su.
A game da yadda ake samun karuwar gudanar da harkokin kasuwanci ta hanyar yanar gizo ta wajen saye da kuma sayarwa ba tare da an shiga harbar banki wajen aika ko karbar kudi ba, tuni NCC ta kulla yarjejeniya da Babban Bankin Najeriya (CBN) a game da wannan batu.
“A game da yadda ake hada-hadar kasuwanci a yanar gizo ta sa NCC da CBN suka hada karfi wajen ganin kamfasnonin sadarwa ba sa zaluntar al’umma”.
“Ta ce NCC da CBN suna kokarin fito da tsarin da zai ba jama’a damar ganin sun kulla huldar kasuwanci a tsakaninsu da bankuna da kuma kamfanonin sadarwar ba tare da ana zaluntarsu ba. A game da haka ne NCC da CBN za su fito da ka’idojin da yakamata bankuna da kamfanonin sadarwar su rika bi don dorewar shirin, da zarar an kammala komai za a sanar da duniya”, inji ta.
Daraktar ta kara da cewa a kan haka ne Hukumar NCC take taka muhimmiyar rawa wajen fadakar da al’umma a game da sanin hakkokinsu.
Ta ce a game da bayanan da suka tattara, an gano cewa a da kimanin mutum 500 ne kadai suka san yadda ake aika lambar da ke hana su karbar sakannonin da ba sa bukata daga kamfanonin sadarwa, amma kawo yanzu an samu kimanin mutum miliyan 10 da suka aika lambar da ke hana karbar sakonnin da ba sa bukata. “Don haka ya dace a jinjinawa Hukumar NCC a game da wannan batu. Yanzu muna kokarin ganin kamfanonin sadarwar ba sa cire kudin da suka wuce kima ga kwastomomi don haka muka kayyade musu farashin da za su rika cazar al’umma.
“Haka kuma mun kayyade mafi karancin farashin da yakamata kamfanonin sadarwar su rika cazar al’umma. Don haka muna da sashen da ke lura da yadda kamfanonin suke cazar kwastomominsu da kuma mafi karancin farashin da yakamata su rika karba. Don haka duk wanda ya saba ka’ida zai iya fuskantar hukunci daga NCC”.
Ta kara da cewa an kafa Hukumar NCC ce saboda al’umma don haka za ta yi duk mai yiwuwa wajen kare hakkin al’umma daga kamfanonin sadarwar. Ta ce a kan hake ne NCC take hulda kai tsaye da kamfanonin maimakon amfani da ’yan kamasho. “An kafa Hukumar NCC ce saboda al’umma, don haka za mu ci gaba da kare wa al’umma hakki daga kamfanonin sadarwar don ganin kwalliya tana biyan kudin sabulu a bangaren sadarwa”, inji ta.
Ta ce a kan haka ne NCC take shirya tarurrukan fadakar da al’umma irin tarukan fadakar da al’umma na “The Consumer Parliament” da taron “The Consumer Town Hall” da kuma taron “The Consumer Outreach”. Ta ce baya ga tarurrukan da aka lissafa a sama sai kuma Hukumar ta kirkiro da taron shiga karkaka don ganawa da su fuska-da-fuskta don jin irin matsalolin da suke fuskanta daga wajen kamfanonin sadarwar. “Don haka ne muka daina amfani da dillalai (masu shiga tsakani) wajen hulda da jama’a, muka gwammace mu rika tuntubar al’umma kai tsaye don jin irin kalubalen da suke fuskanta a wajen kamfanonin sadarwar da suke hulda da su”. Ta ce yanzu an samu rangwame a game da yadda al’umma ke biyan kudin kira da na karbar sakonni (SMS) saboda yadda gasa ke wanzuwa a tsakanin kamfanonin sadarwar. Ta ce gasar ce ta sanya farashin kira ko na karbar sakonni (SMS) ra ragu, inda al’umma suka samu rangwame.