NCC ta amince wa kamfanonin sadarwa ƙara kuɗin kira da data
Za a ƙarin kuɗin kira zuwa fiye da Naira 18 duk minti yayin da kuɗin data zai haura Naira 400 duk Gigabyte ɗaya.
Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta amince wa buƙatar kamfanonin sadarwa na ƙara kuɗin kiran waya da data a ƙasar.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Reuben Mouka ya fitar a yammacin wannan Litinin.
- Amurka jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance — Trump
- An rantsar da Donald Trump a matsayin Shugaban Amurka na 47
NCC ta ce ta bayar da izinin ƙarin ne bisa ga ikon da take da shi a ƙarƙashin tanadin sashe na 108 na Dokar Sadarwar Najeriya, 2003 (NCA).
NCC ya ce matakin na zuwa ne domin daidaitawa da kuma amincewa da farashi da kuma cajin kuɗaɗen da kamfanonin sadarwa ke yi.
Sanarwar ta ce kamfanonin sadarwa sun miƙa wannan buƙata ne sakamakon yanayin da ake samu a kasuwa.
“Ƙarin, ba zai wuce kashi 50 cikin 100 ba, duk da cewa ya yi ƙasa da sama da kashi 100 cikin ɗari da kamfanonin sadarwa suka nema, ya zo ne bisa la’akari da sauye-sauyen da za su yi tasiri ga ɗorewar kasuwanci,” in ji sanarwar
Hukumar ta ƙara da cewa “Ba a yi ƙarin farashin kuɗin kirar waya ba tun 2013, duk da ƙarin tsadar gudanar da ayyukan yau da kullum da kamfanonin sadarwa ke fuskanta.
“Wannan ƙarin da aka amince da shi yana da zummar magance babban giɓin da ake da shi tsakanin tsadar gudanar da al’amura da kuma kuɗin kira a halin yanzu tare kuma da tabbatar da cewa an biya wa masu amfani da waya buƙatunsu.”
Hukumar ta kuma tabbatar da cewa an yanke wannan shawarar ne bayan tattaunawa mai zurfi da manyan masu ruwa da tsaki a sassan gwamnati da masu zaman kansu.
A bayan nan ne dai rahotanni suka bayyana cewa kamfanonin sadarwar Nijeriya za su yi ƙarin kuɗin kira zuwa fiye da Naira 18 duk minti yayin da kuɗin data zai haura Naira 400 duk Gigabyte ɗaya.