NCC ta ba kamfanonin sadarwa awa 48 su yanke layukan da ba a amfani da su
Hukumar Sadarwar Najeriya (NCC) ta ba kamfanonin sadarwa awa 48 domin ta yanke layukan da aka musu rajista amma ba a amfani da su. Daraktan hulda da jama’a na hukumar, Tony Ojobo ne ya sanar da hakan a Jihar Legas, inda ya ce ci gaba da rajistan layuka da kamfanonin ke yi ya taimaka wajen […]
Hukumar Sadarwar Najeriya (NCC) ta ba kamfanonin sadarwa awa 48 domin ta yanke layukan da aka musu rajista amma ba a amfani da su.
Daraktan hulda da jama’a na hukumar, Tony Ojobo ne ya sanar da hakan a Jihar Legas, inda ya ce ci gaba da rajistan layuka da kamfanonin ke yi ya taimaka wajen rage ta’addanci.
Da yake jawabi mai taken : Bibiyan ainihin bayanan mutane da sauqaqe harkar kasuwanci a Najeriya, a lokacin taron jami’an hulda da jama’a, ya ce sanin ainihin bayanan mutane zai taimaka wajen sauqaqe kasuwanci.
A cewarsa: “Duk da matsalolin da ake samu, lamarin shi ne duk mai amfani da waya dole ya yi rajista, inda zai bayar da bayanai da suka hada da cikakken bayanin mutum kamar rajstan haihuwa.
“Rajistan ’yan qasa yanzu yana cikin ayyukan samar da cigaba mai daurewa na shekarun bayan 2015, bayan an samu mutane sama da biliyan 2.4 da ba su wani yadda za a gane su, kuma wadannan mutanen suna zaune ne a yankin Afirka da Asia.
“Duk da cewa asalin yadda ake gane mutum shi ne ta hanyar lambobin sirri irinsu password da PINs da sauransu, amfani da hoton shatan hannu da qwayar ido ya fi nagarta da aminci. An fi amfani da su a duniya wajen yin lasisin tuqi da shaidar shiga qasa.
“Hoton shatan hannu ya fi aminci wajen gano wanda ya aikata wani abu. Shi yasa jami’an tsaro suka fi amfani da shi wajen yaqi da ta’addanci.”
Daga nan sai ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kula sosai da bangaren tattara bayanai na qasar, domin a cewarsa samar da cikakken manhajar tattara bayanai wanda masu sha’awar zuba jari za su gani zai taimaka wajen samar da yarda da aminci.