NCC ta ci tarar kamfanin CWG Naira miliyan 25
Hukumar Sadarwa ta Kasa ta ci tarar kamfanin CWG PLC, kamfanin da ke sadarwa da bayanai, Naira miliyan 25 domin saba ka’idojin hukumar sadarwa ta kasa. Hukumar Tsara wa Kamfanonin Sadarwa ta ce dole ta tilasta wanda suka kauce wa ka’idojinta na karo na biyu na shekara ta binciko DCC Satelite Limited ta ba da […]
Hukumar Sadarwa ta Kasa ta ci tarar kamfanin CWG PLC, kamfanin da ke sadarwa da bayanai, Naira miliyan 25 domin saba ka’idojin hukumar sadarwa ta kasa.
Hukumar Tsara wa Kamfanonin Sadarwa ta ce dole ta tilasta wanda suka kauce wa ka’idojinta na karo na biyu na shekara ta binciko DCC Satelite Limited ta ba da takardar izininta ga CWG wanda hakan ya saba wa Hukumar Sadarwa ta Najeriya na sashe na 38 na kundin dokar 2003.
Hukumar NCC ta bayyana wannan a bayanan tilastawa.
Sashen doka na 38 ya bayyana duk wanda ya yi haka, “bada takardan izini na mutum daya ne sai dai idan Hukumar Sadarwa ta ba da dama daga wani kamfani zuwa wani a rubuce. Hukumar ta bukaci su biya Naira miliyan 25 kawai ga kamfanin CWG daga tsarin hukumar na sashe na 14 na (e) da na (f) da na (g) da kuma na (i) na hukumar ga wanda ya saba ka’idojin shekarar 2005, matakin Hukumar, NCC ta bayyana haka ga hukumar.
Hukumar ta ce ta gano kamfanoni guda 24 wadanda suka kasa sabunta izzinin da aka ba su bayan izininsu ya kare kuma an ba da sanarwa su sabunta.
Hukumar ta bayyana cewa kamfanoni biyar kawai suka sake sabunta takardunsu sauran kanmfanoni 19 kuma hukumar ta ba da damar daukan mataki a kansu.
NCC ta ce wasu kamfanonin sadarwa sun saba wa ka’idojin samar da kayan aiki da tsarinsu.
Ta ce tuni ta ba da izini ga kamfanonin MTN da HIS da ATC da Airtel da kuma Globacom da su gyara kayan aikinsu don kada su fuskanci fushin hukumar.