NCC ta rage tarar da ta ci MTN

A jiya Alhamis ne Hukumar da ke Sanya Ido a kan Kamfanonin Sadarwa (NCC) ta bayyana cewa ta rage tarar da ta ci kamfanin MTN daga Dala biliyan biyar da miliyan 200 zuwa Dala biliyan uku da miliyan 400. Hakan dai na nufin an rage tarar da kusan ninki uku.A wata sanarwa da kamfanin MTN […]

NCC ta rage tarar da ta ci MTN
NCC ta rage tarar da ta ci MTN

A jiya Alhamis ne Hukumar da ke Sanya Ido a kan Kamfanonin Sadarwa (NCC) ta bayyana cewa ta rage tarar da ta ci kamfanin MTN daga Dala biliyan biyar da miliyan 200 zuwa Dala biliyan uku da miliyan 400. Hakan dai na nufin an rage tarar da kusan ninki uku.
A wata sanarwa da kamfanin MTN ya fitar, ya ce hukumar ta bukace shi ya biya tarar kafin karshen watan nan, kamar yadda kafar yada labarai ta Premium Times ta bayyana .
Har ila yau, Shugaban Kamfanin a Najeriya Michael Ikpoki ya ajiye aikinsa. Hakazalika, a farkon watan jiya ne Shugaban Kamfanin a Duniya Baki daya Mista Sifiso Dabengwa ya yi murabus nan-take, yana mai cewa ya dauki matakin ne “domin kare martabar kamfanin da masu zuba jari a cikinsa.”
Kamfanin ya ce zai fara tattaunawa da NCC nan take domin duba yiwuwar fara biyan tarar.
A watan Oktoba ne NCC ta sanya wa MTN tarar Dala biliyan biyar da miliyan 200 saboda ya ki yanke layukan mutanen da ba su yi rijista ba har wa’adin da aka diba domin yin rijistar ya cika. Wasu masana suna ganin hakan yana da nasaba da ziyarar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake yi a kasar Afirka ta Kudu, wadda ita ce ta mallaki kamfanin.
MTN shi ne babban kamfanin sadarwa a Najeriya, kuma ana ganin ‘yan ta’adda na yin amfani da layukan wayoyi domin tsara kai hare-hare.