NCC ta sadaukar da shekarar 2017 ga abokan hulda

A ci gaba da kokarin tabbatar da bada kariya ga abokan hulda don samun fa’ida da kuma alfanun kudadensu a harkokin sadarwa, Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) ta gabatar da tsarin tattaunawa da abokan huldar a dukkan yankunan kasar nan baki daya. Manufar wadannan tattaunawar da hukumar ta fara a wannan shekara ta 2017 da […]

NCC ta sadaukar da shekarar 2017 ga abokan hulda

A ci gaba da kokarin tabbatar da bada kariya ga abokan hulda don samun fa’ida da kuma alfanun kudadensu a harkokin sadarwa, Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) ta gabatar da tsarin tattaunawa da abokan huldar a dukkan yankunan kasar nan baki daya.

Manufar wadannan tattaunawar da hukumar ta fara a wannan shekara ta 2017 da abokin huldar ita ce domin ilmantarwa, fadakarwa, karin haske da kuma sanin dukkan bayanan da suka dace gare su a matakin can kasa. Shirin da ya haifar da samuwar Zauren Abokan Huldar Wayar Sadarwa wato Telecommunication Consumer Parliament (TCP da Tsarin Albishir ga Abokan Hulda wato Telecom Consumer Outreach Programme (COP) da kuma Babban Taron Gama-gari da Abokan Huldar Sadarwa (CTM).

Hukumar ta kwashe kimanin watanni tana aiwatar hakan wajen sadar da bayanai ga abokan hulda a dukkan sassan kasar nan. Haka kuma ta inganta sababbin shirye-shirye don tabbatar da cewa an baiwa abokan hulda cikakkiyar kariya, muhimman bayanai da kuma ilmantarwa (PIE). Tsarin na ‘PIE’ zai maida hankali ne wajen gamsar da kishin ruwansu game da sababbin tsare-tsare da suka hada da zauren abokan huldar sadarwa, tsarin albishir ga abokan hulda, da kuma babban taron gama-gari da abokan huldar sadarwa ta hanyar shafin musamman na yanar gizo, musayar ra’ayi a shafukan intanet irin su Twitter da Facebook da kuma amsa bukatun abokan hulda kyauta ta hanyar kirar lambar NCC ta kar-ta-kwana 622, sannan da kuma fitowa cikin shirye-shiryen rediyo don ilmantar da abokan hulda a game da ‘yancinsu da damarmaki da kuma sabon tsarin musayar ra’ayi da mutanen dake zaune a karkara.

Babu ko shakka cewa samar da bayanai shi ne babban sinadarin ci gaban al’ummar dake zaune a biranai ko karkara, da yadda dukka mai himma, kokari, karrashi ko kungiyar da ta san abinda ta key i, ba za su yi watsi da dumbin adadin mutanen karkara ba. A yayin da yake magana a madadin Mataimakin Babban Sakataren NCC, Farfesa Umar Danbatta a lokacin Babban Taron Gama-gari da Abokan Huldar Sadarwa karo na 27 a Kabba dake Jihar Kogi a kwanan nan, Mataimakin Daraktan Kula da Harkokin Abokan Hulda, Alhaji Isma’il Adedigba ya bayyana cewa masayar ra’ayi da abokan huldar zai taimaka wajen bunkasawa, tallafawa da kuma karin haske musamman akan shirin nan na kiran lambar 2442 don kawo karshen sakonnin banza dake shigowa wayoyin al’umma da kuma ilmantar da su ‘yancinsu ta yadda za su warware dukkan barazanar da suke fuskanta a wayoyin sadarwarsu.

Haka kuma ya ce tuni wadannan tattaunawan za su kasance ne kasuwanni da masallatai da majami’u da bankuna da kuma wuraren taruwan jama’a a dukkan yankuna shida na Tarayyar Najeriya. “An kaddamar da wannan shekara ta zama ta abokan huldar sadarwa ce. Wannan kamfe ne da ake don tabbatar da cewa kowa ya samu cikakken bayani akan yadda ake amfani da lambobin 2442 don dakile sakonni mara amfani ga wayoyin jama’a. zamu iya cewa ma wannan tattaunawa ta fara kasancewa a kasuwanni da masallatai da majami’u da bankuna da wuraren taruwan jama’a a yankunan karkara. Mun fara aiwatar da wannan shiri a daukacin yankunan nan shida na kasar nan baki daya. An gabatar da guda a Kaffi makon jiya, sannan an aiwatar da wasu a Kudu maso gabas da dukkan sassan nan shida dake kasar nan,” a cewarsa.

Mista Adedigba ya kara da bayyana alfanun babban taro na gama-gari da al’umma cewa manufar ita ce don samun damar hada dukan bangarorin uku, tsakanin abokan hulda, ma’aikatan da kuma ma su sarrafa al’amuran sadarwar don kawo karshen dukkan matsalolin da ake fuskanta a baya game da wayoyin sadarwa don kara samun ilimi kan yadda za a yi amfani da lambobin NCC na 622 da 2442 don shigar da dukkan korafi na dakatar da tarkacen sakonnin da ka iya shigowa, don magance matsalar, ingantawa da kuma tabbatarwa.

Haka zalika a yayin taron, Daraktan Kula da Harkokin Abokan Hulda, Abdullahi Maikano ya bayyana cewa manufar hauduwar ita don tabbatar da cewa abokan hulda sun amfana da kudadensu wajen samun cikakken sakamako sannan zai kasance kuma a matsayin wata madafar hukumar ta tuntuba don samun damar shiga tsakani don kare hakkin abokan hulda wajen samu kyawun ayyukan sadarwa da su kansu ma su sarrafa ayyukan da kamfanonin baki daya. Ya kuma kara da cewa hukumar ta maida hankali ne don tabbatar da cewa kwastoma ya samu irin ingancin da ake bukata, ya fahimci dukkan bayanai da cikakken ilimi akan sha’anin don magance faruwar asara da dukkan zabin fai’idar da ta kamata a yayin amfanin da wayoyin sadarwa.

Abu ne sananne cewa samar da wannan azure na tattaunawa don fadakar kwastoma shine kokoluwan matakin da ya kamata a dauka don bada kariya gare su daga cuta ko zalunci. Domin wannan hukuma ba za ta zuba ido ga dukkan wata kumbiya-kumbiyar da za ta haifar wa kwastoma wata barazana a yayin amfani da kuma samun kyakkyawan yanayin sadarwa daga kamfanonin sadarwa dake ba shi  sabis. Dukkan wadannan ba za su samu ba face ta hanyar bayar da bayanai da kuma ilmantarwa, a bisa wannan manufa ne NCC ta tashi haikan wajen ilmantar da kwastomomi don kare su daga dukkan cuta, da sakonnin yaudara da kuma dukkan salon damfara na sakonnin neman aiki da sauransu. Domin kwastoma bas hi da ikon sanin ka’idojin yarda tsari kafin tsunduma kansa ciki, amma wannan zai bas hi damar sanin kowane lungu da sako na manufar tsari kafin ya zuba kudinsa ciki.

Wannan hukuma karkashin shugabanta, Farfesa Umar Dambatta, ta na amfani da dukkan tsare-tsare da kuma samar da zaurukan ilmantarwa tare da taimakon kamfanonin sadarwa don baiwa abokan hulda cikakkiyar kulawa tamkar sarakai, bisa la’akari da ’yanci da kuma damarmakin su. A yayin ayyana wannan shekara a matsayin ta abokan hulda ce dungum, wannan hukuma ta yunkura wajen tabbatar da cewa kimanin ma su amfani da wayoyin sadarwa miliyan 154 dake Najeriya sun samu cikakken kula da kuma daraja ta musamman wajen sanar da su dukkan bayanai, hakkoki, garabasa, zabi da kuma iko.

NCC ta dauki haramar karfafa kwastomomi ta hanyar sababbin dabaru akan wayoyinsu wato Mobile Network Operators (MNO) da hanyoyin Intanet na Internet Serbice Probiders (ISP) da kuma sabon tsarin da ya kunshi magance matsalolin kwatoma da dukkan korafinsa ta hanyar sakon kar-ta-kwana wato Short Message Serbices (SMS) don ba su damar sarrafa kowane tsari.