NCC ta umarci a sake buɗe layukan mutane da aka rufe
Hukumar ta umarci kamfanonin su sake bai wa mutane damar haɗe layukansu da lambar NIN.
Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), ta umarci kamfanonin sadarwa da su sake buɗe layukan wayar mutane da suka rufe.
NCC, ta ce mutane ba su samu isasshen lokaci wajen haɗa lambar shaidar ɗan ƙasarsu ta (NIN) da layukan wayoyinsu ba.
- Zanga-zanga: Gwamnatin Katsina ta kira taron gaggawa
- Majalisa za ta yi zaman gaggawa kafin zanga-zangar yunwa
Hukumar ta ce sake buɗe layuka ba zai ɗauki lokaci ba, amma zai bai wa mutane damar sake haɗa layukansu da lambar NIN ɗinsu.
Mutane da dama sun gaza amfani da layukansu sakamakon kulle su da kamfanonin sadarwa irin su MTN, Airtel, Glo da 9Mobile suka yi a ƙarshen mako.
Sai dai rufe layukan na cikin manufar gwamnati na buƙatar duk masu amfani da waya dole su haɗa NIN ɗinsu da layukansu.
An fara haɗa lambar NIN da layin waya a watan Disamban 2020.
An ɗage wa’adin rufe haɗa lambar da layukan waya zuwa ranar 31 ga watan Yuli, 2024, domin bai wa mutane damar yin rajistar.
Duk da wannan tsawaita lokaci, mutane da dama ba su haɗa lambar NIN da layukan wayoyinsu ba.
Manufar gwamnati ita ce inganta tsaron ƙasa da tabbatar da samun bayanan ’yan ƙasa da ke amfani da layukan waya.
Haɗa lambar NIN da layukan wayoyi na taimakawa wajen tabbatar da ainihin bayanan mutane.
NCC ta kira ga waɗanda ba su kammala haɗa layukansu da lambar NIN ba da su gaggauta yi domin gujewa sake toshe layukansu.
Rahotanni da ke fitowa daga wasu yankuna, sun nuna yadda aka yi wa ofishin kamfanin sadarwa na MTN cikar ƙwari a safiyar ranar Litinin.
Lamarin ya kai wasu ga bai wa hammata iska, kan ganin an sake buɗe musu layukan da aka rufe.