NCC: Yanzu ne lokacin da ya dace a zuba jari a bangaren sadarwa a Najeriya

Hukumar Sadarwar Najeriya (NCC) ta ce yanzu ne lokacin da ya fi dacewa a zuba jari a bangaren sadarwar Najeriya. Babban mataimakin shugaban hukumar, Farfesa Umar Garba Danbatta ne ya sanar da hakan a Abuja, a lokacin da jami’an ofishin jakadancin Amurka suka kawo masa ziyarar aiki, inda ya ce ya kamata ‘yan kasashen waje […]

NCC: Yanzu ne lokacin da ya dace a zuba jari a bangaren sadarwa a Najeriya

Hukumar Sadarwar Najeriya (NCC) ta ce yanzu ne lokacin da ya fi dacewa a zuba jari a bangaren sadarwar Najeriya.

Babban mataimakin shugaban hukumar, Farfesa Umar Garba Danbatta ne ya sanar da hakan a Abuja, a lokacin da jami’an ofishin jakadancin Amurka suka kawo masa ziyarar aiki, inda ya ce ya kamata ‘yan kasashen waje su shigo Najeriya domin yanzu kasar ta samu lafiya a bangaren kasuwanci.

Sai ya fada wa jami’an na ofishin jakadancin karkashin jagorancin Rachael Atwood Mendiola da su ba masu zuba jari ‘yan Amurka shawara da su zo su zuba jari a bangaren sadarwar Najeriya.

“Muno so masu zuba jari su shigo bangaren sadarwar Najeriya. Ina da tabbatacin cewa za su ci riba cikin sauri. Yanayin kasuwancin ya kara habbaka sosai, mun samu tsaro matuka, sannan kuma Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin bayar da tallafi ga wadanda za su zuba jari.

“Sannan kuma muna da wajen da ke bukatar wannan bangaren sosai. Har yanzu muna da bangarori kusan 200 da ba su da damar sadarwa. Wanda hakan ya yanke kimanin mutum miliyan 400, ciki har da mutane a karamar Hukumar da na fito a Kano. Don haka ‘yan kasuwa za su iya shigowa su yi amfani da wannan damar,” inji shi.

A bangaren kula da harkar fasahar bangaren (OTTI), Shugaban Hukumar ya ce ba a fara kula da wannan fasahar ba tukuna a Najeriya.

Fasahar OTTI, wata manhaja ce kamar Facebook, Whattsapp, 2go, Instagram da sauransu da ake amfani da su wajen isar da sako ga jama’a.

“Masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa suna cewa mu yi wani bu a kan bangaren OTTI, domin suna amfani da manhajarsu suna samun kudi, amma zai yi wuya mu yi wani abu a yanzu,” inji Farfesa Danbatta.

Shugaban na NCC ya ce ya yi magana da hukomomin kula da harkokin sadarwa a Amurka da wasu kasashe, inda suka shaida masa a hakaikaice cewa ba za a iya yin komai ba a yanzu.