NCC za ta kara kwanakin cin gajiyar sauran Data zuwa mako 2

Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC), za ta kara tsawon lokacin da za a rika amfani da Datar da ta saura ga masu amfanin da ita zuwa kwana 14. Sai dai kungiyar Masu Harka da Kamfanonin Sadarwa ta kasa (NATCOMS), ta ce kwanakin ba su wadatar ba, maimakon haka kungiyar ta bukaci a kara wa’adin zuwa […]

NCC za ta kara kwanakin cin gajiyar sauran Data zuwa mako 2

Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC), za ta kara tsawon lokacin da za a rika amfani da Datar da ta saura ga masu amfanin da ita zuwa kwana 14.

Sai dai kungiyar Masu Harka da Kamfanonin Sadarwa ta kasa (NATCOMS), ta ce kwanakin ba su wadatar ba, maimakon haka kungiyar ta bukaci a kara wa’adin zuwa kwanaki 30.

 Shugaban kungiyar NATCOMS, Cif Deolu Ogunbanjo, ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Legas, inda ya bayyana shawarar karin kwana 14 a matsayin abin maraba, ya ce amma hakan bai wadatar ba, idan aka lura da halin da tattalin arziki ke ciki, inda masu saye ba su morar kudinsu game da Data da suke amfani da ita.

 “Ya kamata Hukumar NCC ta bayar da tsawon kwana 30 ne maimakon 14, saboda halin da tattalin arziki ke ciki. Wani yana iya haduwa da matsi ko gasa kan bukatar iyalai, amma bai da kudin da zai sake saye a cikin kwana 14. Wa’adin kiran waya da aka sa kati shi ne kwana 90, don haka bai kamata sayen Data ya zama daban ba,” inji Shugaban kungiyar NATCOMS.

Babban Mataimakin Shugaban Hukumar NCC, Farfesa Umar dambatta, ya ce za a ba masu saye kwana 14 su ci gajiyar abin da suka saya koda ba su sabunta a ranar da wa’adin Datar za ta kare ba.

dambatta ya ce, wannan zai dakatar da abin da ake yi a yanzu, inda mai saye zai yi asarar sauran Datarsa idan ya gaza sabunta wata a ranar da wa’adin wadda ya saya ya kare.

A cewarsa, Hukumar NCC ta san cewa harkokin sadarwa suna da matukar muhimmanci ga ci gaban kasar nan. “Hukumar NCC ta kuma lura sosai cewa, masu amfani da harkokin sadarwa sun cancanci su rika ci gajiyar darajar kudinsu. Hukumar NCC ta kuma fahimci cewa akwai bukatar a rika mu’amala da masu amfani da harkokin sadarwar a matsayinsu na muhimman masu ruwa-da-tsaki a al’amuran sadarwa, musamman a abin da ya shafin bangaren gudanar da ayyuka. Idan zan iya tunawa a cikin muhimman batutuwa takwas na shugabancina, batun karfafawa da kare masu sayen kaya ko hulda da kamfanonin sadarwa ne yake mataki na shida. Manufar wannan kudiri ita ce a kare abokin hulda daga cutarwa ta hanyar samar da cikakkun bayanai da ilimantarwa don fahimatarwa kan zabin da ake da shi wajen amfani da hanyoyin sadarwar zamani,” inji shi.