NCC za ta kwace lasisin wasu kamfanonin wayar sadarwa
Wasu daga cikin manyan jami’an Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) tare da manyan jami’an tsaro na kasar nan sun yi zama da wakilan kamfanonin sadarwar wayoyi shida da aka samu da laifukan boye lambobin waya tsakanin abokan hulda. A yayin tattaunawar, wadda ta gudana a ofishin hukumar na Abuja, inda wakilan jami’an tsaron suka tunkari […]
Wasu daga cikin manyan jami’an Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) tare da manyan jami’an tsaro na kasar nan sun yi zama da wakilan kamfanonin sadarwar wayoyi shida da aka samu da laifukan boye lambobin waya tsakanin abokan hulda.
A yayin tattaunawar, wadda ta gudana a ofishin hukumar na Abuja, inda wakilan jami’an tsaron suka tunkari kamfanonin sadarwar bisa hujjoji game da zargin da hukumar ta NCC ke yi gare su, amma duk da haka an sake ba su karin lokaci don kare kansu daga zargin kamar yadda jaridar Daily Trust ta lakanta.
Kamar yadda dokar ayyukan sadarwa ta Najeriya da kuma tsarin gudanarwarta ta shimfida, cewa an bai wa kamfanonin lasisin gudanarwar har zuwa 31 ga watan Janairun wannan shekarar, don nuna dalilan da suka sanya hukumar za ta kwace lasisi ko dakatar da ayyukan kamfanin, bisa dalilan samun sa da wannan laifi kamar yadda hukumar da kuma jami’an tsaron suka tsara, a cewar jami’an.
“Bisa ga hadarin dake tattare da wannan dabi’a game da tsaro da zaman lafiyar kasa da kuma harkokin masu amfani da wayoyi, wannan hukuma ta sha alwashin kwace lasisin dukkan kamfanin da aka samu cikin irin wannan haramtaccen aiki. Domin ba za mu taba tsiraita sirrin kasar mu ba ta kowace fuska. A game da haka kuma, akwai hukunci mai tsanani gare su idan ma har laifin nasu bai shafi soke lasisi ba,” in ji wani jami’in hukumar, wanda ya lakanci lamarin.
Haka kuma an bayyana cewa hukumar ta na taka-tsantsan wajen kiyaye dokokin sadarwar kamar yadda suke, don gudun wani kamfani ya yi korafi kan rashin adalci, don haka hukumar ke shirin bayyana hukuncin da ya dace a bayyane.
Hukumar ta NCC ta kuduri aniyar bayyana hukunce-hukuncen da za ta aiwatar kan dukkan kamfanin da ya sa kansa cikin wannan badakala ta boye lambar wayoyin masu amfani, musamman na kasashen waje.
Haka zalika wani jami’i ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa, za a hukunta kamfanoni da yawa ta hanyar tara ko kwace lasisi sakamakon wannan laifi.
An kuma tabbatar da cewa akwai yiwuwar a hukunta wadannan kamfanonin da abin ya shafa nan da makonni kadan masu zuwa. Kodayake Daily Trust ta ruwaito a kwanan nan cewa za a hukunta kamfanonin sadarwar wayoyi guda shida da aka samu da wannan laifin a watan Fabrairun wannan shekarar.
A daya bangaren kuma, kamar yadda hukumar sadarwar ta tattaro ra’ayoyi daga masu amfani da wayoyi, ya nuna cewa an samu raguwar yawan amfani da boyayyen lamba daga abokan hulda. Wannan kuma babbar nasara ce ga irin kokarin da hukumar ta ke yi don kawo karshen wannan dabi’a, in ji hukumar.
“Sakamakon haka, ba za mu rika daukar abubuwa da wasa ba. Sannan zamu ci gaba da sanya ido tare da lura da ayyukan gidajen sadarwa gwagwardon fadi ko tsukewarsu a cikin ayyukansu. Duk wanda aka samu da wani laifi dole a hukunta shi gwargwadon yadda doka ta tanada,” in ji NCC.
Kamfanonin sadarwar guda shida da aka samu da wannan laifin sun hada da Medallion Communications Limited da Interconnect Cleaning House Nigeria Limited da Niconnd Communication Limited da Breeze Micro Limited da Solid Interconnectibity da kuma Edchange Telecommunications Limited.