NCC za ta shirya bita kan sabuwar dokar sadarwa a Kano

A lamarin da ya shafi kara fadada harkokin jin ra’ayi daga abokan hulda da kuma al’amuran masu ruwa da tsaki don inganta kyawawan ayyukan sadarwa; Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) za ta gudanar da taron bita a ranar 15 ga Fabrairun wannan shekara, game da nagartar gudanarwa a masana’antar sadarwa.  Taron Kano wanda shi ne […]

NCC za ta shirya bita kan sabuwar dokar sadarwa a Kano

A lamarin da ya shafi kara fadada harkokin jin ra’ayi daga abokan hulda da kuma al’amuran masu ruwa da tsaki don inganta kyawawan ayyukan sadarwa; Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) za ta gudanar da taron bita a ranar 15 ga Fabrairun wannan shekara, game da nagartar gudanarwa a masana’antar sadarwa. 

Taron Kano wanda shi ne karo na uku na wannan bitar wayar da kai da hukumar ta shirya a daukacin yankuna shida na kasar nan. Na farkon shi ne aka kaddamar a Legas 11 ga watan Agustan 2017 sai kuma na biyu da aka gudanar a Enugu ranar 16 ga Nuwamba, 2017; yayin da na Kano za ta zama shiyya ta uku dake karbar bakuncin wannan bita.

Sabuwar dokar gudanarwar gwamnati ta masana’antar sadarwa, wacce aka gabatar a watan Yulin 2014, sannan aka yi gyare-gyare a 2016, ta bada mafi karancin hazakar da ake bukata don cike gibin dake da akwai da tsare-tsare da kuma bangaren nagartar ayyukan kamfanonin sadarwar wayoyi.

Dokar wacce aka faro ta bisa zabin kai, amma daga bisani aka maida ita wajiba ta fuskar sanya ido da kuma hurumin aiwatarwa.

Taron bitar ta Kano za ta fuskanci harkokin masu ruwa da tsaki na yankin Arewa maso Yamma da kuma manufar hukumar na jin ra’ayoyin jama’a, kamar yadda ta ziyarci kamfanoni da masu gudanarwar da kuma masu ruwa da tsaki a daukacin yankin.

Babban bako mai jawabi a taron shi ne Shugaban kungiyar Lauyoyi na Najeriya (NBA), Alhaji A.B. Mahmoud (SAN). Yayin da Shugaban NCC, Sanata Olabiyi Durojaiye da kuma Babban Mataimakin Shugaban NCC, Farfasa Umar Garba Danbatta za su kasance masu masaukin baki.