NDLEA a Bayelsa ta kama mutum 70 da muggan kwayoyi
Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun kwayoyi (NDLEA) a Jihar Bayelsa ta bayyana nasarar wani kasurgumin kamu da ta yi na masu laifuka daban-daban da hukumar ke yaki da su a jihar, a samamen da ta rika kai wa lokuta daban-daban a fadin jihar. Ta ce kimanin mutum saba’in ne suka shiga hannunta, ciki har […]
Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun kwayoyi (NDLEA) a Jihar Bayelsa ta bayyana nasarar wani kasurgumin kamu da ta yi na masu laifuka daban-daban da hukumar ke yaki da su a jihar, a samamen da ta rika kai wa lokuta daban-daban a fadin jihar. Ta ce kimanin mutum saba’in ne suka shiga hannunta, ciki har da wani da ake zargi sojan Najeriya ne.
Kwamandar hukumar a jihar ce, Uwargida Josephine Obi ta bayyana wa manema labarai haka a Yenagoa. Ta ci gaba da fayyace wadanda aka kama da cewa shida daga cikinsu sun same su ne da laifin fataucin muggan kwayoyi, ganyen tabar wiwi da kuma garin wani sinadari mai illar gaske da ke sanya maye.
Shugabar ta ce an kama mutum 24 tsakanin watan Janairu Yuli, sauran mutum 18 kuma da aka kama an gurfanar da su gaban kotu. Haka kuma wasu mutum tara an kama su ne a watan Janairu na bana, yayin da karin wasu mutum hudu a watan Maris, wasu mutum bakwai kuma a watan Afirilu na bana.
A cewarta, “sama da kilo 55.6 na tabar hodar iblis muka kwace da kilo 4.3 na hodar hiroyin da damin tabar wiwi mai nauyin kilo 97.233, sai kuma wata hoda mai suna Satiba mai nauyin kilo 1.463.2.”
Da aka tambaye ta game da sojan da ake zargi, ta ce hukumarta ta aike wa hukumar sojan Najeriya bayanin haka domin a gano gaskiyar lamarin.