NDLEA ta kafa cibiyar kula da masu shaye-shaye a Yobe 

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta  kafa karamar cibiyar kula da muggan kwayoyi a Damaturu babban birnin jihar Yobe.

NDLEA ta kafa cibiyar kula da masu shaye-shaye a Yobe 

Jami’an hukumar NDLEA

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta  kafa karamar cibiyar kula da muggan kwayoyi a Damaturu babban birnin jihar Yobe.

Kwamandan hukumar a Jihar, Abdulazeez Ogunboye  ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Damaturu a wani bangare na bikin ranar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya ta shekarar 2025.

Ogungboye ya kara da cewa cibiyar wacce tun daga lokacin da ta fara aiki na daya daga cikin nasarorin da hukumar ta samu a jihar.

“An shigar da mutane tara da suke ta’ammali da muggan kwayoyi a cibiyar, daga cikin su an samu nasarar gyara halayyar mutum takwas halayyar su, an sallame su tare da sake haduwa da iyalansu, yayin da daya ke ci gaba da karbar hoton gyaran hali.

“Daya daga cikinsu yanzu haka ya samu tallafin fara gudanar da harkokin kasuwanci don dogaro da kai tare da watsar da waccar mummunar dabi’a ta ta’ammali da muggan kwayoyi,” in ji Ogunboye.

Kwamandan ya ce bisa la’akari da tsadar ayyuka a cibiyar, hukumar ta hada kai da masu hannu da shuni a jihar domin taimaka wa a wannan kokarin gyaran halim masu ta’ammali da kwayoyin.

Kwamandan ya kuma shawarci masu shaye-shaye a kananan hukumomi 17 na jihar da su tuntubi kwamandojin shiyya na hukumar da ke kusa da su kan yadda za su shiga wurin, wanda ya ce shi ne irinsa na farko a tarihin jihar.