NDLEA ta kama dilolin kwaya 100, ta fasa dabar shaye-shaye 14 a Kaduna
An dilolin kwaya maza da mata sun shiga hannu a garin Zariya da kuma Kaduna
Dillalan miyagun kwayoyi guda 100 sun shiga hannu, a yayin da aka tarwata matattarar masu shaye-shaye 14 a Jihar Kaduna a cikin mako hudu da suka gabata.
Kwamandan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) a Jihar Kaduna, Umar Adoro, ya ce dillalan miyagun kwayoyin da jami’an hukumar suka kama sun hada da maza 93 da mata bakwai.
- NAJERIYA A YAU: Kalubalen ’Yan Takarar Shugabancin Najeriya A 2023
- ’Yan sanda sun cafke matashi kan zargin kashe uwa da danta a Adamawa
- Atiku: Ruwa ba sa’an kwando ba ne – Sakon PDP ga Tinubu
Ya bayyannan cewa an kama dilallan miyagun kwyoyin da kuma tarwatsa wuraren da ake shaye-shayen ne a samamen da hukumar ta kai a garin Zariya da kuma Kaduna a cikin wata Mayu da ya gabata.
Ya ce bayyana cewa unguwannin da aka tarwatsa matattarar masu shaye-shayen miyagun kwayoyin sun ha hada da Abakwa da Malali da Tirkaniya da Rigasa da Romi da Filin Misata a garin Kaduna.
Sai kuma unguwannin Chikaji da Sabon Gari da sauransu da ke Karamar Hukumar Zariya.