NDLEA ta kama mutum 26 kan zargin safarar kwayoyi a Gombe

An kuma kama dilolin da wasu kwayoyi masu yawa

NDLEA ta kama mutum 26 kan zargin safarar kwayoyi a Gombe

NDLEA

Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama wasu mutum 26 da ake zargin da safarar kwayoyi a Jihar Gombe.

Hukumar ta kuma ce ta sami nasarar kama kwaya mai nauyin kilogram 2.654.

Jami’in hulda da Jama’a na hukumar a jihar, Henry E. Ihebuzor, ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya raba wa manema labarai a Gombe.

Ya ce hukumar ta samu nasarar ce a wani samame na musamman da ta gudanar bisa umurnin Shugaban hukumar na kasa Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya

Ya love kwayoyin da aka kama sun hada da Tabar Wiwi mai nauyin kilogiram 2.570 da kuma wasu kwayoyin masu nauyin kilogiram 84.

Hukumar ta gargadi dilolin kwaya da masu sayarwa a jihar da su guji wannan sana’a don gudun fuskantar fushin hukuma, inda yace idanun su na kowanne lungu da sako dan magance harkar miyagun kwayoyin.