NDLEA ta kama tsofaffi suna safarar kwayoyi a Borno

Hukumar NDLEA ta kama wani dan shekara 70 da abokinsa mai shekaru 65 kan safarar miyagun kwayoyi a Jihar Borno.

NDLEA ta kama tsofaffi suna safarar kwayoyi a Borno

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama wani dan shekara 70 da abokinsa mai shekaru 65 kan safarar miyagun kwayoyi a Jihar Borno.

Kakakin NDLEA na kasa, Femi Babafemi ya ce an kwace allurori 32,000 na kwayra Tamadol a hannunsu tsofaffin da dububsu ta cika.

Femi Babafemi ya ce asirin tsofaffin ya tonu ne bayan an kama wasu matsa biyu abokan hulɗars a yankin Gamboru a jihar Borno.

Jami’in ya ce a ranar Asabar din kuma jami’an hukumar suka cafe wani wani dan shekara 24 dauke da curi 40 na tabar wiwi a Jihar Yobe, a hanyarsa ta kaiwa Jamhuriyar Nijar.

A jihar Kano kuma jami’an NDLEA sun kama wani dan shekara 35 da kilogram 62 na tabar wiwi; wani dan shekara 28 da kwalabe 244 na kwayar Kodin.

Hakazalika hukumar ta kama wani dan shekara 28 da kwayar Tramadol guda 49, 800 a ranar Alhamis.

Femi Babafemi, Director, Media and Advocacy of NDLEA said this on Sunday in a statement in Abuja Abuja.

Hukumar ta kuma kama wani direba da kwakaye 40 na kwayar Kodin guda 8,4000 a Jihar Kaduna.

Akwai kuma wani direba da aka kama ya boye tabar wiwi a injin motarsa a Jihar Osun.

A jihar ce kuma aka kama wata macce mai shekara 26 da ke hada wata ƙwayar mai suna skuchies, wanda aka kama lita 16 na kwayar da kuma tabar wiwi a hannnunta.