NDLEA ta kama wani da ya hadiye kullin kwayoyi 80 tare da wasu 64

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya, NDLEA, ta kama wasu mutum 64 da ake zargin masu safarar kwayoyi ne, maza 55 sai kuma mata 9 a cikin wadanda aka kama akwai wani mutum mai shekaru 55 mai suna Kouassi Jean Paul wanda aka fi sani da Eze Ikechukwu. Eze Ikechukwu, ya […]

NDLEA ta kama wani da ya hadiye kullin kwayoyi 80 tare da wasu 64

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya, NDLEA, ta kama wasu mutum 64 da ake zargin masu safarar kwayoyi ne, maza 55 sai kuma mata 9 a cikin wadanda aka kama akwai wani mutum mai shekaru 55 mai suna Kouassi Jean Paul wanda aka fi sani da Eze Ikechukwu.

Eze Ikechukwu, ya hadiye kullin kwayoyi 80 duk a cikinsa, Hukumar ta kuma kama wasu masu tabin hankali 54 daga watan Janairu zuwa Agusta 2019. Kamar yadda Kwamandan NDLEA Garba Ahmadu ya sanar.

Kwamandan ya sanar da hakan ne a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, a lokacin da ake binciken fasinjojin Najeriya da zasu ta shi a jirgin saman Ethiopian Airline zuwa filin jirgin saman Jakarta da ke kasar Indonesiya.