NDLEA ta kama ’yan kwaya 78 da kilogiram 113 na kwayoyi a Sakkwato
Hukumar Yaki da sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama ’yan kwaya 78 da kilogiram 113 na miyagun kwayoyi daga watan Janairu kawo wannan lokacin a Jihar Sakkwato. Kwamandar hukumar a Jihar, Iro Muhammad ne ya bayyana hakan a wani taron da manema labarai, don murnar zagoyowar bikin ranar yaki da sha […]
Hukumar Yaki da sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama ’yan kwaya 78 da kilogiram 113 na miyagun kwayoyi daga watan Janairu kawo wannan lokacin a Jihar Sakkwato.
Kwamandar hukumar a Jihar, Iro Muhammad ne ya bayyana hakan a wani taron da manema labarai, don murnar zagoyowar bikin ranar yaki da sha da fataucin kwayoyi da aka gudanar ranar Talata.
- Dalilin da ya sa na yi watsi da shawarar cire tallafin mai – Buhari
- Kiristoci masu ziyarar ibada daga Najeriya sun isa Jordan
Ya ce cikin kayan mayen da hukumar ta gano, akwai kilo gram 91 na Tabar Wiwi da wasu magunguna ciki har da Kodin da suka kai lita 63.
Ya kuma ce hukumar ta sami nasarar gurfanar da mutum 12 a tsakanin wannan lokacin, hadi da horar da ’yan kwaya 58 da ‘yan uwansu suka kawo su don gyaran hali.
Kwamandan ya kuma ce manufar bikin ita ce wayar da jan al’umma kan illolin shan miyagun kwayoyi.