NDLEA ta kama ’yar Afirka ta Kudu da hodar iblis a Abuja
Matar ta yi ƙoƙarin amfani da ɗanta mai shekara uku a matsayin kariya domin kauce wa cikakken binciken jami’an tsaro.
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta kama wata ’yar ƙasar Afirka ta Kudu mai shekara 38, Jessica Ann, da ake zargi da safarar hodar iblis mai nauyin kilogiram 5.75 ta Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Hukumar ta ce matar ta yi ƙoƙarin amfani da ɗanta mai shekara uku a matsayin kariya domin kauce wa cikakken binciken jami’an tsaro.
- Sojoji sun kama mota maƙare da miyagun ƙwayoyi a titin Legas zuwa Calabar
- Mun gano ’yan ƙasashen waje a cikin mayaƙan ISWAP — Sojoji
Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Ya ce an kama wadda ake zargin ne a ranar Litinin, 6 ga watan Yuli, yayin tantance fasinjojin da suka iso da jirgin Qatar Airways daga Doha na ƙasar Qatar.
A cewarsa, da farko matar ta musanta mallakar jakunkunan da aka gano hodar iblis ɗin a cikinsu.
Sai dai bayan jami’an NDLEA sun tabbatar cewa alamun da ke jikin jakunkunan sun yi daidai da bayanan da ke fasfot ɗinta, ta sauya maganarta tare da amincewa cewa jakunkunan nata ne.
Ta kuma yi iƙirarin cewa ta manta cewa ita ce ta yi rajistar jakunkunan kafin tafiyar.
Sanarwar ta ce matar ta bayyana cewa ta taso ne daga Cambodia ta biyo ta Doha kafin ta iso Abuja.
NDLEA ta ce bayanan sirri da suka taimaka wajen cafke ta sun nuna cewa tana cikin wata ƙungiyar ƙasa da ƙasa da ke safarar miyagun ƙwayoyi tare da mijinta ko abokin zamanta, Jan Coenraad De Jager.
A cewar hukumar, mutumin yana zaune ne a Cambodia, inda ake zargin sukan shirya safarar miyagun ƙwayoyi daga ƙasar zuwa Afirka ta Kudu ta hanyoyin sadarwar ƙungiyar.
