NDLEA ta tsare ‘yan sanda 2 akan rakiyar makamai
Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA), ta tsare wasu jami’an ‘yan sanda biyu akan tuhumarsu da laifin rakiyar bindigogi dubu 1,250. A wata sanarwa da kakakin Hukumar NDLEA Mista Jonah Achema ya fitar ya ce, jami’an hukumar sun kwato makaman ne lokacin da suke bakin aiki a garin Gwagwalada da ke hanyar […]
Kullen COVID-19 ya sa masu shan kwaya sun karu, inji NDLEA
Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA), ta tsare wasu jami’an ‘yan sanda biyu akan tuhumarsu da laifin rakiyar bindigogi dubu 1,250.
A wata sanarwa da kakakin Hukumar NDLEA Mista Jonah Achema ya fitar ya ce, jami’an hukumar sun kwato makaman ne lokacin da suke bakin aiki a garin Gwagwalada da ke hanyar Abuja zuwa Lokoja.
Rahoton na bayyana cewa, an tura sakon karban makaman ne ta amfani da kamfanin sufurin motoci daga jihar Legas wanda ‘yan sanda ne zasu karbi sakon.
‘Yan sandan biyu su ne, Jacob Jalwap, mataimakin Sufuritandan ‘yan sanda da ke aiki a Hedkwatar ‘yan sanda ta Jos babban birnin jihar Filato da kuma Kopora Nandul Seizing, da ke aiki a ofishin ‘yan sanda na Angua Rogo a Jos, an kuma kama su a Jos bayan binciken da aka lokacin da suke rakiyar makaman.