…Ndume ya dace da Shugabancin Majalisar Dattawa – Maizabura
Al’ummar Arewa maso Gabas na ci gaba da kiraye-kiraye da nuna bukatar a ba su mukamin Shugabancin Majalisar Dattawa, wanda suka ce yankin bai taba yi ba, kuma suna ganin hakan zai taimaka wajen warware matsalolin yankin. Wani fitaccen dan siyasa a Jihar Borno, Alhaji Umar Muhammad Maizabura ya shiga cikin mutanen da suke kiran […]
Al’ummar Arewa maso Gabas na ci gaba da kiraye-kiraye da nuna bukatar a ba su mukamin Shugabancin Majalisar Dattawa, wanda suka ce yankin bai taba yi ba, kuma suna ganin hakan zai taimaka wajen warware matsalolin yankin.
Wani fitaccen dan siyasa a Jihar Borno, Alhaji Umar Muhammad Maizabura ya shiga cikin mutanen da suke kiran a bar wa yankin wannan kujera a wannan karo, inda ya ce, yanki ya samu koma baya tare da fuskantar wariya daga Gwamnatin Tarayya, tare da bayyana Sanata Muhammde Ali Ndume da wanda ya fi dacewa da shugabancin majaliasar.
Alhaji Umar Maizabura ya ce yankin ne mafi koma-baya a kasar nan ta yadda babu wata masana’antar da za ta tallafa wa dimbin matasan yankin da aikin yi, wanda hakan ya taimaka wajen tabarbarewar tsaro da rikicin Boko Haram ya daidaita shi.
Alhaji Maizabura ya ce ya kamata a ba yankin Shugaban Majalisar Dattawa, domin a samu saukin warware matsalolin da yankin ya dade yana fama da su, saboda shugaban zai fahimtar da gwamnati irin matsalolin da suka addabe ta ta yadda za a ceto yankin cikin kankanen lokaci. Alhaji Maizabura ya ba Jam’iyyar APC shawarar ta zabo mutum nagari mai gaskiya da rikon amana da sanin makamar aiki, kamar Sanata Muhammad Ali Ndume, “Domin mu al’ummar Jihar Borno mun san Ali Ndume mutum ne mai gaskiya da rikon amana da sanin makamar aiki da taimakon al’umma, kuma ya san matsalolin da suke addabar yanki, don haka muna rokon shugabannin siyasa da abin ya shafa su duba wannan al’amarin domin ceto wannan yankin, ta yadda zai san ana yi da shi kuma ya farfado daga magagin mutuwar da yake yi sakamakon wariya daga Gwamnatin Tarayya,” inji shi.
Yanzu haka dai mutum uku ne 3 ne ake ambatar cewa suna bukatar hawa wannan kujera ta Shugaban Majalisar Dattawa daga Arewa maso Gabas, wadanda suka hada da Sanata danjuma Goje daga Jihar Gombe da Sanata Ahmed Lawan daga Jihar Yobe da Sanata Muhammad Ali Ndume daga Jihar Borno.