NECAS za ta kai manoman da suka ki biyan rance kotu
Shugaban shirin bayar da rancen noma (NECAS) na shiyyar Arewa maso Gabas, Alhaji Ahmad Muhammad Dukku, ya ce NECAS za ta kai karar manoman da suka ki dawoda rancen noman da aka ba su. Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa, inda ya ce ba su da niyyar kai […]
Shugaban shirin bayar da rancen noma (NECAS) na shiyyar Arewa maso Gabas, Alhaji Ahmad Muhammad Dukku, ya ce NECAS za ta kai karar manoman da suka ki dawoda rancen noman da aka ba su.
Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa, inda ya ce ba su da niyyar kai karar manoma har sai manoman sun yi taurin kai wajen kin dawo da bashin da suka ba su.
Alhaji Ahmed Dukku, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa (RIFAN) ta Jihar Gombe, ya ce bukatarsu ita ce manoman su biya rancen don a samu damar bai wa wadansu manoman bashi.
“Mun rubuta musu takarda inda muke umartar su da su dawo da bashin don wadansu su samu. Idan ba a biya ba, ba mu da kudin da za mu bai wa wadansu manoman,” inji shi.
Alhaji Dukku ya ce a bara, NECAS ta bai wa manoma dubu 280 rancen noma; amma manoma dubu shida ne kawai suka fara dawo da nasu bashin. Ya ce NECAS ta bai wa kowane manomi kudi tsakanin Naira dubu 170 zuwa dubu 200 idan ka hada yawan manoman za su ba da adadin kudin da ake bin manoman a Gombe.
Shugaban ya ce, a nasu ra’ayin ba sa son ci gaba da bayar da rancen har sai an biya na baya, amma Shugaban Kasa Buhari yana son a kara bayar da rancen, saboda kara inganta samar da abinci a kasa musamman noman shinkafa.
Daga nan sai ya yi kira ga manoman da suka karbi bashin NECAS su daure su dawo da shi a gama komai cikin lumana ba sai an je kotu ba.