NECO: Dalibai sun shiga zullumi bayan Ganduje ya tsaurara sharadin daukar nauyin jarabawa
Gwamnati ta tsaurara sharadin daukar nauyin dalibai kwanaki kalilan kafin rufe rajistar jarabawa
Iyayen daliban sakandare sun shiga damuwa bayan Gwamnatin Jihar Kano ta tsaurara sharadinta na daukar nauyin daliban da za ta biya wa kudin zana jarabawar NECO.
Iyaye da dalibai na tsoron za su iya yin biyu babu bayan gwamnati ta sanya samun Kiredit 9 a matsayin sharadin daukar nauyin daliban da za su zana jarabawar.
- Mata miliyan 37 ne ba sa samun audugar al’ada a Najeriya
- Mafarauta sun kashe Kwamandojin Boko Haram a Borno
Dalibai da iyayensu sun shiga wannan tashin hankali ne ganin yadda dalibai aka fadi sosai a jarabawar da dalibai za su samu gurbi domin gwamnati ta biya musu kudin jarabawar.
A gefe guda kuma gwamnatin jihar ta sanar cewa yanzu daliban da suka samu Kiredit 9 ne kawai za ta dauki nauyi, matakin da iyayen suka bayyana a matsayin tamkar fafe gora a ranar tafiya.
A shekarar 2021 dai, Kredit bakwai ake bukata daga dalibi, ciki har da darusan Lissafi da Ingilishi, kafin gwamnatin jihar ta biya mishi kudin jarabawar kammala sakandare. Amma ta ce daga yanzu sharadin ya koma Kiredi tara.
Sakamakon jarabawar samun gurbin da Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta fitar a ’yan kwanakin da suka gabata ya fito ne kwanaki kadan kafin rufe rajistar jarabwar NECO ga dalibai masu kammala sakandare.
Hakan ne ke barazana ga iyayen da ’ya’yansu ba su da Kiredit tara, ta yadda za su samu kudi su biya wa ’ya’yan nasu cikin dan kankanin lokaci.
Irin wannan matsala ce iyayen dalibai suka yi fama da ita a shekarar 2021, lokacin da gwamnatin jihar ta ce ta kara yawan Kiredit din da dalibi zai ci kafin ta dauki nauyin jarabawarsu, daga biyar ta mayar da shi Kiredit bakwai.
Binciken Aminiya ya gano a hukumanci kudin rajistar jarabawar NECO N21,500 ne, amma makarantu na karbar 23,500 zuwa N25,000 saboda wadansu hidindimu da suka dangaci rajistsar jarabawar.
Wakilinmu ya kuma gano daliban da suka rubuta jarabawar da gwamantin jihar ta shirya sun fadi.
Misali, daga Makarantar Sakandaren Tarauni da ke garin Kano, dalibai 475 ne suka zana jarabawar, amma mutum uku ne kacal suka samu Kiredit tara da gwamnatin jihar ta shardanta.