NECO ta fitar da jadawalin jarabawar 2020

NECO ta sanar da yadda dalibai za su samu jadawalin jarabawar da kuma ranakun da za a kammala

NECO ta fitar da jadawalin jarabawar 2020

Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) ta fitar da jadawalin jawabarta na 2020 ga dukkanin dalibai da ke rubuta jarabawanta.

Shugaban NECO Farfesa Godswill Obioma yayin kaddamar da jadawalin a ranar Talata ya ce hukumar za ta sa kyamarorin lura da take-taken jama’a a cibiyoyi da ma’adanar takardun jarabawar domin kawar da magudi.

Farfesa Obioma ya ce NECO za ta gudanar da jarabawarta na kammala sakandare (SSCE) daga ranar Litinin 5 ga Oktoba zuwa 18 ga watan Nuwamba, 2020.

Ta kammala karamar sakandare kuma za a rubuta ta ne daga Litinin 24 ga Agusta zuwa 7 ga Satumba, 2020.

Masu kammala karamar sakandare da suka samu matsala a jarabawar darussan lissafi da Turancin Ingilishi za su maimaita a ranakun 11 da 12 ga watan Nuwamba.

Su kuma ‘yan ajin karshe a makarantar firamare za a yi tasu jarabawar a ranar 17 ga watan Nuwamba.

— Yadda za dalibai za su samu jadawalin NECO

Shugaban hukumar ya shawarci masu rubuta dukkanin jarabwar NECO da su sauke jadawalin daga shafin hukumar www.neco.gov.ng.

“Za a rufe rajistar jarabawar BECE kwana uku kafin a fara rubutawa, ta NCEE kuma kwana bakwai kafin a fara sai SSCE da za a rufe yin rajista 10 ga watan Satumba”, inji shi.

Dalibai 80,110 suka yi rajistar yin jarabawar NCEE, wasu 104, 341 za su yi BECE sannan 169,144 za su rubuta jarabawar SSCE.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos