NEDC ta ba da kayan agaji ga wadanda ambaliyar Maiduguri ta shafa

Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC) ta raba kayan agaji ga waɗanda bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a Maiduguri, Jihar Borno.

NEDC ta ba da kayan agaji ga wadanda ambaliyar Maiduguri ta shafa

Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC) ta raba kayan agaji ga waɗanda bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a Maiduguri, Jihar Borno.

Manajan Daraktan Hukumar, Mohammed Goni Alkali, ya ce, “Mun tura tallafin  buhunan shinkafa 200,000 da kwalin  taliya 150,000.

“Sauran sun haɗa da manyan jarkokin man girki 250,000, da barguna 200,000, tabarmi 200,000,  rigunan yara 65,000, da gidajen sauro 20,000 da sauransu a jihohin Arewa maso Gabas.”

Alkalin ya kara da cewa, hukumar za ta yi amfani da tsarin mazabun  siyasar yankin Arewa maso Gabas, wanda ya kunshi gundumomin sanatoci 18, da mazabun majalisar wakilai 48, da kuma mazabu na jiha 1,024, wajen raba kayan agaji ga wadanda bala’in ambaliyar ruwa ta shafa a kowace jiha a yankin.

Dangane da rugujewar madatsar ruwa ta Alau, Alkali ya ce tuni hukumar ta bayar da kwangilar gyarawa da sake gina madatsar ruwan kafin afkuwar ambaliyar ruwa.

To sai dai, saboda da abin da ya faru a baya-bayan nan, hukumar za ta sake duba kwangilar domin sake gyara gine-ginen madatsun ruwa da ambaliyar ruwa ta lalata.

An mika kayan tallafin ga gwamnatin jihar ne a dakin ajiyar kayayyakin abinci na hukumar ta NEDC da ke Maiduguri.

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato