Neja Tornadoes ta sake haurawa gasar rukunin Firimiya ta kasa
Kulob din Neja Tornadoes da ke Minna ya samu nasarar hayewa gasar rukuni-rukuni na Najeriya da ake wa lakabi da Nigeria Professional Football League (NPFL) bayan ya zama zakara a rukunin da ya fafata..  Kulob din ya samu nasarar haka ne bayan ya lallasa kulob din Mighty Jets da ke Jos a ranar Asabar da […]
Kulob din Neja Tornadoes da ke Minna ya samu nasarar hayewa gasar rukuni-rukuni na Najeriya da ake wa lakabi da Nigeria Professional Football League (NPFL) bayan ya zama zakara a rukunin da ya fafata..  Kulob din ya samu nasarar haka ne bayan ya lallasa kulob din Mighty Jets da ke Jos a ranar Asabar da ta gabata da ci 2-0.  Wasan ya gudana ne a filin wasa na Bako Kwantagora da ke Minna.  Kulob din ya fafata ne a rukunin da suka hada da kungiyoyi bakwai ciki har da na Gombe United da ABS da kuma na Maighty Jet da ke Jos.
A shekarar 2012 ne kulob din ya koma gasar rukunin ’yan dagaji (amateur) bayan kulob din Rising Stars ya lallasa shi da ci daya mai ban haushi a wasan karshe.    Sai ga shi a wannan karo kulob din ya sake komawa gasar rukunin firimiya bayan ya samu nasara a kan Mighty Jets.
’Yan kwallon Tornadoes biyu Yakubu Alfa da Samson Adeyemi ne suka jefa kwallaye biyu a ragar Mighty Jets da hakan ya ba kulob din damar komawa gasar rukunin firimiya ta kasa.