NEMA ta bayyana jihohi 14 da za su iya fuskantar mummunar ambaliya a makon nan
NEMA ta ce za a yi ambaliyar ne daga 4 zuwa 8 ga watan Yuli
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta bayyana wasu jihohi 14 da ta ce akwai yuwuwar a sami mummunar ambaliyar ruwa a cikinsu nan ba da jimawa ba.
A cewar hukumar, ana fuskantar barazanar samun ambaliyar ce daga tsakanin 4 zuwa 8 ga watan Yulin 2023 a yankuna 31 da ke cikin jihohin.
Gargadin dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ko’odinetanta na shiyyar Legas, Ibrahim Farinloye, ya fitar ranar Laraba.
A kan haka ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a jihohin da lamarin ya shafa da su dauki matakan da suka dace domin kiyaye rayuka dukiyoyin jama’a.
Hukumar ta ce yankunan sun hada da:
Filato: Langtang, Shendam
Kano: Sumaila, Tudun wada
Sakkwato: Shagari, Goronyo, Silame
Delta: Okwe
Kaduna: Kachia
Akwa Ibom: Upenekang
Adamawa: Mubi, Demsa, Song, Mayo-belwa, Jimeta, Yola
Katsina: Katsina, Jibia, Kaita, Bindawa
Kebbi: Wara, Yelwa, Gwandu
Zamfara: Shinkafi, Gummi
Borno: Briyel
Jigawa: Gwaram
Kwara: Jebba
Niger: Mashegu, Kontagora
Ibrahim Farinloye ya kuma yaba wa Sashen Gargadi Kan Ambaliya (FEWS) na hukumar na Ma’aikatar Muhalli ta Kasa da ke Abuja saboda fitar da bayanin a kan lokaci. (NAN)