NEMA ta raba Tan dubu 4, 905 na kayan abinci
A tsakanin watannin Yuni zuwa Satumbar wannan shekarar ce Gwamnatin Tarayya a karkashin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (NEMA) ta raba kimanin Tan 4,905 na kayayyakin abinci ga masu gudun hijirar da ke zaune a Jihohi 6 na yankin Arewa maso Gabas. Bayanin haka na kunshe ne a wata sanarwa da Shugaban Hukumar NEMA Alhaji […]
A tsakanin watannin Yuni zuwa Satumbar wannan shekarar ce Gwamnatin Tarayya a karkashin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (NEMA) ta raba kimanin Tan 4,905 na kayayyakin abinci ga masu gudun hijirar da ke zaune a Jihohi 6 na yankin Arewa maso Gabas.
Bayanin haka na kunshe ne a wata sanarwa da Shugaban Hukumar NEMA Alhaji Mustapha Maihaja ya fitar a ranar Juma’a 13 ga watan Oktoba, 2017 a Abuja.
Ya bkayyana haka ne a lokacin da yake jawabi awajen taron Ranar kokarin Rage Aukuwar Bala’a Ta Duniya na wannan shekara mai taken: “Muhimmancin samar da zaman lafiya, yunkurin kaucewa daga aukuwar yin gudun hijira.”
A nata jawabin a yayin taron, Dokta Habiba Lawal, Mukaddashin Sakataren Gwamnatin Tarayya ta ce taken taron na bana ya zo a kan gaba idan aka yi la’akari da yadda ake yawan samun masu gudun hijira ta hanyar ambaliyar ruwa da kuma fadade-fadace a wannan kasa tamu.
Dokta Habiba Lawal wacce ta samu wakilci daga Sakataren Dindindin da ke ofishinta Mista Roy Ugo, ta ce idan aka yi la’akari da yadda ake yawan samun ambaliyar ruwa da tashe-tashen hankula daga kungiyar Boko Haramda kuma a fadace-fadacen kabilanci musamman a yankin Arewa maso Gabas to yunkurin da ake yi na ganin an rage aukuwar bala’i musamman a Najeriya ya zo a kan gaba.
Ta ce wannan yunkuri da ake yi tamkar ci gaba ne a kan shawarar da aka bayar a taron da aka yi a Sendai da Majalisar dinkin Duniya ta shirya a watan Maris din 2015. A taron, an bayar da shawarar hanyoyin da suka kamata a bi ne don ganin an rage aukuwar bala’o’i da kuma rasa rayuka, da inganta tattalin arziki da kula da muhalli da kuma samar da abubuwan jin dadin more rayuwa a kowane bangare na duniya nan da shekarar 2030. Ta ce a kan haka ne ake yunkurin ganin an rage aukuwar bala’i a kowane sashe na duniya daga nan zuwa shekarar 2030.