NEMA ta tallafa wa wadanda harin Gombe ya shafa
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta kai tallafin magunguna ga wadanda harin bam na bayan nan ya shafa a tashar mota ta Dadin Kowa da Tashar Dukku da ke garin Gombe fadar Jihar Gombe.Dokta Zainab Chukwuma, wata babbar likita a Asibitin Koyarwa na Tarayya ce ta karbi magungunan a madadin hukumar asibitin, […]
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta kai tallafin magunguna ga wadanda harin bam na bayan nan ya shafa a tashar mota ta Dadin Kowa da Tashar Dukku da ke garin Gombe fadar Jihar Gombe.
Dokta Zainab Chukwuma, wata babbar likita a Asibitin Koyarwa na Tarayya ce ta karbi magungunan a madadin hukumar asibitin, inda ta jinjina wa hukumar bisa wannan agaji.
Dokta Zainab Chukwuma, ta ce tallafin magunguna ya zo a lokacin da ya dace, sai ta gode wa Hukumar NEMA saboda yadda take kula da al’ummar yankin Arewa maso Gabas da suke yawan haduwa da hare-haren maso tayar da kayar baya.
Bayan mika magungunan Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim dankwambo, ya jagoranci tawagar Babban Daraktan Hukumar NEMA Malam Sani Sidi, inda suka ziyarci wuraren da aka kai harin don jajanta wa al’ummar tashohin.
Daga tashoshin motar Gwamna Dankwambo ya zarce unguwannin Tudun Wada da Shamaki da Arawa da kuma Yalanguruza inda ya yiw a ’yan uwan wasu daga cikin wadanda suka rasu a harin kunar bakin waken.
A Unguwar Arawa, Gwamnan ya ba da izini a bude wa ’ya’yan Malam Umar Muhammad Mailemo hudu daya wanda ya rasu a harin asusun ajiya a banki domin zai aiko da Naira dubu 500 a rika biya musu kudin makaranta kada karatunsu ya tsaya tare da aikewa da kayan abinci ga dukkan iyalan wadanda ya ziyarta.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai Gwamnan ya yi kira ga shugabannin tashoshin motar su kara mai da hankali wajen kula da wadanda suke hada-hada a tashar ta tantance su kafin su shiga kuma su mai da hankali wajen yin addu’o’i don kara samun dorewar zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.
Sai ya yi alkawarin zai turo a duba asarar da aka yi a tashohin don duba yadda za a tallafa musu wajen rage asarar da ta same su.
A hare-haren biyu mutum 36 ne suka rasu, yayin da 99 suka samu munanan raunuka inda ake yi musu jinya a asibitocin birnin Gombe.