Neman aure (3)
Wani saurayi ne da abokansa biyu suka je gidan su budurwarsa gaisuwar surukai. Bayan an gaisa sai baban yarinyan ya tambayi daya daga cikin abokan cewa: “Yaya sunanka?” Ya ce: “Sunana Imran.” Sai baban yarinyar ya ce: “To karanta mana Suratul al-Imrana.” Sai ya karanta. Baban ya tambayi dayan cewa: “Kai kuma ya sunanka?” Sai […]
Wani saurayi ne da abokansa biyu suka je gidan su budurwarsa gaisuwar surukai. Bayan an gaisa sai baban yarinyan ya tambayi daya daga cikin abokan cewa: “Yaya sunanka?” Ya ce: “Sunana Imran.” Sai baban yarinyar ya ce: “To karanta mana Suratul al-Imrana.” Sai ya karanta. Baban ya tambayi dayan cewa: “Kai kuma ya sunanka?” Sai ya ce sunanansa Ibrahim. Aka ce masa shi ma ya karanta Suratul Ibrahim sai shi ma ya karanta. Da aka zo kan saurayin yarinyar, babanta ya ce: “Kai kuma ya sunanka?” Sai ya ce: “Sunana Musa amma an fi kirana da Alhamdu.”
Iliyas Idris Fahad Suleja