Neman aure: ’Yan mata da samari a yi hattara
Ina mika godiya ga Allah (SWT) Gagara misali, Mai yin yadda Ya so, ga wanda Ya so, a kuma lokacin da Ya so. Ina yin dubun salati ga Annabi Muhammadu (SAW). Kuma ina rokon Ubangiji Ya yassare fahimtar sakon da nake nufin isarwa cikin wannan mukalar hade da yin amfani da shi ga su wadanda […]
Ina mika godiya ga Allah (SWT) Gagara misali, Mai yin yadda Ya so, ga wanda Ya so, a kuma lokacin da Ya so. Ina yin dubun salati ga Annabi Muhammadu (SAW). Kuma ina rokon Ubangiji Ya yassare fahimtar sakon da nake nufin isarwa cikin wannan mukalar hade da yin amfani da shi ga su wadanda abin ya shafa.
Na shirya yin nan-gida-nan-zaure, game da ’yan mata da samari kan yadda suke neman aure. Idan har ana so batun neman aure ya tafi daidai, dole sai an daki jaki, kuma an daki taiki, wato a taba bangaren samari da ’yan matan.
Don haka a wannan maudu’in zan yi magana a kan abin da ya jibanci kasassabar da ’yan mata da samari suke yi wajen neman aure, sannan na fahimtar da su illolin da kasassabar za ta haifar musu. Na sha jin samari na hira suna son su auri macen da za ta tarairaye su, matan kuma kan ce suna son su auri mijin da zai yi farin ciki da farin cikinsu gami da yin bakin ciki da bakin cikinsu. Kana suna so mijin ya zamo mai kulawa da kyautatawa gare su. Ya tsare musu mutunci, ya kuma ba su duk wani hakkinsu da ya rataya a wuyansa, a lokaci guda samari na kudurin su samu mace saliha, mai tarbiyya, ladabi, biyayya da kuma natsuwa. Amma duk da wannan furucin da wadannan bangarori suke yi, kadan daga cikinsu ne suke tsayawa da natsuwa don tantance wadanda za su yi musu hakan.
Inda za ku yarda da maganata shi ne, akasarin samari da ’yan mata sun fi damka wa zuciyarsu ikon zabar abokan zama a gidan aure, kowa ya san zuciya ba ta da kashi, bugu-da-kari zuciya tana son duk wani abu na kawa da ado ne. To yaya kuke tsammanin za su samu abokan zaman nagari har su rika yin kuka da kukansu? A lokacin da ’yan mata suka ba zuciyarsu damar zaben abokin zama idon zuciyar na kallon wanda ya kasance gwani wajen iya kwalliya, mai dukiya, mai mulki, mai nasaba da kuma iya kalamai, a lokaci guda idon zuciyar takan makance wajen kallon mai addini da tsoron Allah. To yaushe kuke tunanin soyayyar da ba a gina ta domin Allah ba a kuma samu abin da ake so? Haka yake ga bangaren samari, sai idonsu ya rufe har su rika fadi-tashi wajen neman mace mai kyau, nasaba, ko mulki, ko mai dukiya, inda har wadansu ke auren jari, don kawai son duniya. Idan haka ne yaya saurayi zai samu kwanciyar hankali bayan ya yi aure? Bayan ya san ya yi auren ne don wata manufa ba don Allah ba?
A wani lokaci mata su suke bayar da kansu, wanda hakan ke ba maza kofofi da tagogin yaudararsu, dalilin kuwa shi ne, matan kan rudu da kalaman samari, kwalliyarsu, kyawunsu, dukiyarsu, nasabarsu da kuma mulkinsu, inda suke mantawa da baki ya fi sarewa zaki, kudi kuwa kan iya karewa, haka ma mulki ma ba a tabbata a kansa. To yaya wacce ta rudu da wadannan abubuwa daga karshe ba za ta yi da-na-sani-ba?
Haka sai ka ga saurayi ya dage wajen kambama kyawun mace, ko murya ko kudinta, shi ma idanunsa sun shagala ga abubuwan da na ambato a sama, duk saurayin da ya yi haka, to karshe zai yi kuka da idanunsa, domin kwalliyar aurensa ba za ta biya kudin sabulu ba.
Wani abu da za ku tabbatar da dole mata su yi da-na-sani shi ne, su suke darsa soyayyarsu ga mazaje ba ta hanyar Allah da Annabi ba, domin matan kan yi amfani da sigogin da suka mallaka wajen farautar zukatan maza. Misali yanzu idan mace ta mallaki yalwataccen bakin gashi mai santsi da yalki, kai tsaye za ta yaye shi, idan za ta fita unguwa don mazaje su kalla, su so ta don gashin kanta. Idan kuma ta mallaki kyawawan sigogi, sai ta sanya matsatstsu da shara-sharan tufafi, kana ta fito tana taku dagwas! dagwas! da yin yauki a kwararo, duk don ta ja hankalin maza.
To yaya kuke tunanin duk wanda zai je wajen waccar da ta bayyanar da tsiraici ya kasance mutumin kirki? Ko kuma ya so ta don Allah? Kuma kun san ba mutumin kirkin da zai je wajen waccar da ta fidda tsiraici, tsakaninsu ma tofin Allah tsine ne, ko addu’ar Allah Ya shirye ta, in kuwa haka ne matan ba za su samu mai tarairayarsu da farin ciki da farin cikinsu ba.
Wani lokaci za ka ga samari sun rika yin aron tufafi ko motoci, ko wani abu da zai burge budurwarsu, ba tare da tunanin cewa za su auro ta su kawo ta gidansu ba, idan ta zo gidan ta ga ba abin da suka saba nuna mata tun kafin aure, me suke tunanin zai faru?
A wani lokaci kuma matan da suka sakar wa zuciyarsu zabin masoyi, a kan rude su da kudi, kalamai da duk wani kayan yaki na yaudara, wanda a karshe daga an sansu a ’ya mace, ko an yi musu cikin shege, sai a rabu da su, inda matan kan shiga damuwa da ukuba, kana su fara miyagun kalamai a kan wai namji ba dan goyo da zane ba ne, maza ba su da tabbas, duk wacce ta rike namiji uba za ta mutu marainiya ko kuma ka ji suna fadin maza tabarmar kashi ba su naduwa, sun manta cewa su ne suka fara yaudarar kansu ta hanyar ruduwa da abin da mazajen suke da shi.
Za mu ci gaba