Neman aure: ’Yan mata da samari a yi hattara (2)

A je ma bayan kin bayyanar da sigoginki ga mazaje, kuma ba su san ki ’ya mace ba, har sai da kika yi aure, kina jin daga ya biya bukatarsa da ke za ki samu kulawa da kyautatawar da kike zato? Ke ma kin san yasar da ke za a yi tunda tsiraicinki ko kyawun […]

Neman aure: ’Yan mata da samari a yi hattara (2)
Neman aure: ’Yan mata da samari a yi hattara (2)

A je ma bayan kin bayyanar da sigoginki ga mazaje, kuma ba su san ki ’ya mace ba, har sai da kika yi aure, kina jin daga ya biya bukatarsa da ke za ki samu kulawa da kyautatawar da kike zato? Ke ma kin san yasar da ke za a yi tunda tsiraicinki ko kyawun sigoginki ya gani har ya aura, tun da bukatarsa ta biya sai ya yasar da ke, irin yasarwar da ake yi wa kwauren ganga, bayan an ci moriyarta
Wani lokacin za ka samu ciki ya shiga, amma da yake ba don Allah aka kulla soyayyar ba, ba ruwansa haka zai sake ta ba tare da ya kara komawa ta kanta ba. Idan kuma bai sake ta ba, to ta rika ganin wulakancin duniya buhu-buhu ke nan, zai zamanto ba ruwansa da ba ta abinci da abin sha da duk wani abu da ya jibanci hakan, wanda wasu na yin hakan ne, matsayin ko yanzu kasuwa ta watse dankoli ya ci riba, ma’ana ko yanzu aka rabu to bukatarsa ta biya. Sai ka ga mata suna gidan aure, amma suna ta ramewa kamar kudin guziri, kana taba su, su ce  AI MAZA BA SU DA TABBAS, ta manta ita ta yi uwa, ta yi makarbiya wajen zabar miji, ko don kyawunsa, kudinsa, iya kwalliyarsa, kalaminsa ko mulkinsa.
Ga bangaren samarin da suke auren jari kuwa, za ka ga sun rasa iko a kan matansu, domin matan kan fita a lokacin da suka so, su kuma dawo gida a lokacin da suka so, sai ka ga maimakon su samu natsuwa, sai dai su samu tashin hankali. Wa ya jawo hakan? Su ne tun da suka rudi kansu da auren jari.
 Ga bangaren ’yan mata, kuma wani abu da nake so ku sani shi ne, duk namijin da yake zuwa wajen mace, ya san idan tana sonsa don Allah, ko don wani abu nasa. Koda ya lura don wani abu take sonsa, yakan kasa rabuwa da ita, kasancewar mai son tsuntsu shi ke bin sa da jifa har cikin shekarsa, sai ya zamanto ya yi amfani da wannan abin da take so a wajensa a matsayin kugiyar da zai sarkafe ta, duk da kuwa ya san ba don Allah take sonsa ba. To kuna tunanin zai so ta don Allah? Zai yi wuya hakan ya faru, idan kaddara ta riga fata aure ya shiga tsakani, Me kuke zato? Kina tsammanin zai tarairaye ki, ko ya ba ki ingantacciyar kulawa ko? To idan haka ne kin yaudari kanki. Domin daga ya gamsu da ke, zai iya yasar da ke kamar yadda ake yasar da kwallon mangwaro a juji bayan an tsotse shi.
Yanzu kaddara saurayi ya so ki don kyawunki har ta kai ku ga yin aure, a zatonki shi ke nan zai yi ta tarairayarki? To in ba ki sani ba ki sani, duk wanda ya yi aure don kyau kamar misalin sabuwar riga ce, idan tana sabuwa da kyanta zai rika ji da ita, amma daga ta fara tsufa, ma’ana kyanta ya fara gushewa, to zai ji ta fara gundirarsa, kwanci-tashi zai ji yana bukatar sabuwar riga saboda ta zama tsohuwar yayi.
To kwatankwacin matar da ta bari, kyanta ne ya sa mijinta ya aure ta ba wai don Allah ba ke nan; yau-da-gobe gonar Allah ba mai kure ki, zai ga wacce ta dama ki, ta shanye a fagen kyau, kamar yadda kyanki, ya rude shi haka kyanta zai rude shi, yana samunta, za ki zamo ba kya gabansa. Idan kika kasa hakurin zaman gidan ki yi waje rod, domin tafiyarki don barin gidan ba ta dada shi da kasa ba. Idan kuma kin yi hakurin zaman gidan, to wulakanci a kanki kuma iri-iri kin gamu da shi, saboda ya samu wacce ta fi ki, don haka ko kin tafi ma ke ta shafa. Amma inda a ce don Allah ya aure ki fa? Zai zamanto ko ya auro wata zai gwada yin adalci a tsakaninku.