‘Neman Gwamna bisa dalilin addini ba zai haifar da alheri ga Nasarawa ba’

Yekuwar a samu Gwamna Kirista a Jihar Nasarawa a zaben 2015 da ke tafe ya samu suka daga Babban Sakataren Hukumar Maziyarta Kiristoci na Jihar, Barista Clement Ode, wanda ya nuna takaicin cewa masu wandannan kiraye-kiraye na kokarin mayar da batun siyasa zuwa na addini.Barista Ode, ya ce ya lura a baya-bayan nan an mayar […]

‘Neman Gwamna bisa dalilin addini ba zai haifar da alheri ga Nasarawa ba’
‘Neman Gwamna bisa dalilin addini ba zai haifar da alheri ga Nasarawa ba’

Yekuwar a samu Gwamna Kirista a Jihar Nasarawa a zaben 2015 da ke tafe ya samu suka daga Babban Sakataren Hukumar Maziyarta Kiristoci na Jihar, Barista Clement Ode, wanda ya nuna takaicin cewa masu wandannan kiraye-kiraye na kokarin mayar da batun siyasa zuwa na addini.
Barista Ode, ya ce ya lura a baya-bayan nan an mayar da hankali kan yin kamfe ta hanyar kiraye-kirayen a samu Gwamna Kirista a zaben badi, inda ya ce hakan hadari ne da ka iya jefa jaririyar jihar a cikin bala’i.
Kiraye-kiraye daga yankin Arewacin Nasarawa inda Kiristoci suka fi yawa don ganin an samu Gwamna Kirista na karuwa, inda mabiya addinin Kirista ke nanata cewa lokacinsu ne na Kirista ya zama Gwamna daga shiyyar.
Barista Ode ya ce wannan yunkuri zai dusashe hasken wannan muhimmiyar kujera, domin zai rarraba kan mutanen jihar kowa ya zabi dan addininsa, lamarin da ya ce, zai jefa jihar a cikin matsala a daidai lokacin da take farfadowa daga kashe-kashen kabilancin da aka shafe dogon lokaci ana yi.
 “Gwamnoni biyu na farko, Abdullahi Adamu da Aliyu Akwe Doma sun fito ne daga kabilun Afo da Alago. Duk kabilun ’yan asalin Jihar Nasarawa suna da Kiristoci da Musulmi da masu addinin gargajiya. Adamu Muslim ne haka Doma. Gwamna Umaru Tanko Al-Makura dan kabilar Gwandara ne ya karba daga Doma. Gwandara ma ’yan kasa ne kuma akwai Musulmi da Kirista da addinin gargajiya a cikinsu. Shi ma Al-Makura Musulm ne, kuma wannan tsakaninsa da Ubangjinsa ne. To yaya za a tsoma addini a cikin siyasa,” inji Ode.
Ya ce shugabannin uku sun samu kuri’u daga mabiyan manyan addinan uku da ke jihar, inda ya kara da cewa, “Babu wani addini guda daya daga cikin uku da zai iya tsayawa shi kadai ya samu kujerar Gwamnan Nasarawa ko duk wani mukami.”